✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama wanda ya kashe jariri a Adamawa

An kwace wuka, baka/kibiya, da wasu muggan makamai a hannun wanda ake zargin.

Wani mutum mai shekara 40 ya shiga hannun ’yan sanda bisa zargin kashe wani jariri a kauyen Kadamti da ke Karamar Hukumar Numan, Jihar Adamawa.

Rundunar ’yan sandan jihar ta kuma kwace wuka, baka/kibiya, da wasu muggan makamai a hannun wanda ake zargin.

Jami’in Hulda Da Jma’a na Rundunar ’Yan sandan jihar, SP Sulaiman Yahaya Nguroje ya ce  kashe jaririn ne bayan wani hari da aka kai wa mahaifiyarsa, inda da ta samu munanan raunuka a ranar 29 ga watan Satumban 2022 a kauyen Kadamati.

Sanarwar ta ce “’Yan sanda da ke aiki da sashen Numan da jami’an Operation Farauta da al’ummar Nagari sun zage damtse tare da kama mutumin kan laifin.

“Wanda ake zargin, dan shekara 40, mazaunin kauyen Kpasham, Karamar Hukumar Demsa, an kama shi ne bayan wani rahoto da aka samu.”