✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama shi kan zargin yin luwadi da kananan yara

Dubun wani matashi mai shekara 25 ta cika bayan da aka kama shi kan zargin yi wa kananan yara maza fyade. A ranar Laraba ce…

Dubun wani matashi mai shekara 25 ta cika bayan da aka kama shi kan zargin yi wa kananan yara maza fyade.

A ranar Laraba ce aka gufranar da shi a Kotun Kare Kananan Yara da Hukunta Laifukan Fyade ta Jihar Anambra, kan laifin yin luwadi da kananan yara.

Cajin kotun da aka karanta masa ya kara da cewa, “Ka aikata laifin da ya saba Sashe na 3 sakin layi na 2 na Dokar Cin Zarafin Dan Adam (VAPP) da Jihar Anambra 2017.”

Sai dai kuam ya musanta duk tuhume-tuhumen da ake masa da lalata da kananan yara.

Daga nan lauyan wanda ake zargin ya nemi kotu ta bayar da belinsa, amma ta lauyar bangaren masu kara, Amara Amilo ta ki amincewa.

Alkalin kotun, Genevieve Osakwe ta bayar da umarnin tsare wanda ake zargin sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga Satumba, 2022.