✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama shi da hodar iblis ta biliyan 1 yana kokarin tsallake kasa ta Sakkwato

Ya ce, “Wannan ba karamar nasara ba ce a shiyyarmu, inda ko a kwanakin baya sai da muka kama wani nau’i na Hodar ta Iblis.”

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama wani mai safarar miyagun kwayoyi na kasa da kasa da Hodar Iblis ta kimanin Naira biliyan daya.

Hukumar dai ta ce wanda ake zargin mai suna Nkem Timothy an kama shi ne da kulli 62 na Hodar Iblis din wacce nauyinta ya kai kusan kilogiram 1.550, wacce darajarta ta kai wannan adadin kudin.

Daraktan Watsa Labarai na hukumar, Mista Femi Babafemi wanda ya bayyana hakan ranar Lahadi ya ce an cafke wanda ake zargin ne lokacin da yake kokarin tsallakawa zuwa kasar Algeria ta Jamhuriyar Nijar.

Daraktan ya Ambato Kwamandan hukumar a Sakkwato, Bamidele Segun yana cewa an cafke Nkem ne a kan wani babur, dab da kan iyakar Illela yana kokarin tsallakwa Nijar a kokarinsa na zuwa Algeria, inda a can ne yake zama.

Ya ce an kukkulle hodar ne a wasu ribobin yogot.

“Mun kama shi da wani katin ECOWAS mai dauke da sunan wani mutum daban wai shi Auwalu Audu, amma ya ce mana ainihin sunansa shine Nkem Timothy,” inji Kwamandan.

Ya kuma ce tuni jami’ansa  suka fara fadada bincike domin su gano wanda yake daukar nauyinsa da ma sauran gungun wadanda suke harkoki tare.

Ya ce, “Wannan ba karamar nasara ba ce a shiyyarmu, inda ko a kwanakin baya sai da muka kama wani nau’i na Hodar ta Iblis.”