✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 25 kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Jamus

Jamus na zargin hannun Rasha a cikin lamarin

’Yan sanda a Jamus sun kama mutum 25 a fadin kasar da ake zargi da kasancewa mambobi da kuma masu goyon bayan wata kungiyar masu ra’ayin rikau da ke neman hambarar da gwamnatin kasar.

Ana dai yi wa kungiyar lakabi da Reichsbuerger, wacce hukumomin kasar ke yi wa kallon ta ta’addanci.

Bayanai sun nuna ’yan kungiyar na son hambarar da gwamnatin kasar ta karfin tsiya ne domin su dora jagoransu, wanda ke samun tallafi daga kasar Rasha, a matsayin sabon Shugaban Kasar, a cewar Ofishin Babban Mai Shigar da Kara na Kasar.

Akalla dai jami’an ’yan sanda 3,000 ne suka gudanar da aikin kamen ranar Laraba a a birane 130 da ke jihohi 11 a fadin kasar.

Mai shigar da karar ya ce ana zargin mutanen ne da wani kwakkwaran shiri na kutsa kai ta karfin tsiya zuwa cikin ginin Majalisar Jamus ta hanyar daukar makami.

Ofishin ya kuma ce mutum 22 daga cikin wadanda aka kama ’yan asalin kasar ta Jamus ne wadanda ake zargi da shiga kungiyar da aka kira da ta’addanci, yayin da daya daga ciki kuma dan kasar Rasha ne da ake zargi da goyon bayansu.

Gidan talabijin na Aljazeera ya rawaito cewa akasarin mutanen da aka kama suna dauke ne da makamai, kuma ana zarginsu da yi wa kasar zagon kasa.

To sai dai daga bisani a ranar Laraba, gwamnatin Rasha ta musanta hannun kowanne dan kasarta a yunkurin juyin mulkin.

“Wannan matsalar cikin gida ce ta Jamus, babu hannun Rasha ko kadan a ciki,” inji Dmitry Peskov, mai magana da yawun fadar gwamnatin kasar ta Kremlin.