✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama makaman ‘yan bindiga a Suleja

Bindigogi kirar AK-47 da albarusai samda da 350 ne aka kama a hannun wani dan fashin da dubunsa ta cika

’Yan sanda a Jihar Neja sun kama wani mai safarar makamai da bindigogi kirar AK-47 guda bakwai da albarusai guda 375 a garin Suleja na jihar.

Mutumin ya ce shi ne yake dakon makamai ga wani gungun ’yan fashi da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

“Ni direba ne, amma nakan taimaka wa masu wannan aikin wajen safarar makamansu domin samun karin kudaden da za su taimaka min wajen kula da iyalaina.

“Nakan kai makaman ne ga wani Alhaji da ke zaune a Kaduna, amma wannan karon garin Keffi na Jihar Nasarawa zan kai kayan kafin a sami bacin rana a kama ni a Suleja”, inji wanda ake zargin.

Ya ce an biya shi N80,000 da ya kai kashin farko na makaman, an kuma yi masa alkawarin N150,000 idan ya kai sauran wurin da ake bukata, wanda daga ciki aka ba shi kafin alkalamin N20,000.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Abiodun Wasiu ya ce jami’an sashen yaki da ‘yan fashi na SARS da ke kula da yankin Suleja ne suka cafke mutumin.

Ya ce an kama mutumin ne a wata mota kuma ya amsa cewa shi dan dan kungiyar ‘yan fashin ne da ya kware wajen yi musu safarar makamai.

Kakakin ya ce yanzu haka rundunar ta fadada bincike tare da yunkurin ganin ta kama ragowar ’yan fashin.