✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mai shekara 70 tana safarar kwaya a Edo

Dubun tsohuwar ta cika ne a Karamar Hukumar Obia ta Arewa maso Gabas a jihar.

Wata tsohuwa mai shekara 70 mai suna Misis Beatrice Aigbedion tana daga cikin mutanen da Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama a Jihar Edo, bisa zarginta da safarar wasu miyagun kwayoyi sama da kilo dubu biyar a sassan jihar.

Kakakin Hukumar NDLEA, Femi Babafemi a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce bayan kwashe kwanaki ana sa ido, a ranar Laraba 24 ga Nuwamba jami’an NDLEA sun kai farmaki a wani kantin sayar da kayayyaki da ke Uhiere, a Karamar Hukumar Obia ta Arewa maso Gabas a jihar.

Femi ya ce, ’yan sandan sun kwato jimillar kilo 4,261.5 na tabar wiwi, sannan an kama wani da ake zargi mai suna Ikong Stanley a ranar Talata 23 ga Nuwamba, da kilo 1,240 a wani kantin sayar da kayayyaki da ke Uzebba a Karamar Hukumar Owan ta Yamma a jihar, sai kuma aka kama Misisi Aigbedion a Irrua a ranar Larabar da ta gabata.

An kama maganin tari na kodin da Swinol da Rohypnol yayin da wani dillali, Joseph Onyemaechi, mai shekara 50 aka kama shi a Ikpoba Okha, Upper Sakponba, Benin City, a ranar Juma’a da nau’o’in sinadarai masu nauyin kilo 2.055.

Sai Gabriel Akioya da Isa Sal, da aka kama su a ranar Alhamis 25 ga Nuwamba a Irrua, a Karamar Hukumar Esan ta Tsakiya tare da kodin da Tramadol da Swinol da Rohypnol.