✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mai dafa abinci da ruwan wankan gawa a Akwa Ibom

Jami’an ’yan sanda a Jihar Akwa Ibom sun kama wata mata da ake zarginta da yin amfani da ruwan da aka wanke gawa tana dafa…

Jami’an ’yan sanda a Jihar Akwa Ibom sun kama wata mata da ake zarginta da yin amfani da ruwan da aka wanke gawa tana dafa abincin sayarwa da shi.

Matar mai suna Gloria Edet na sana’ar sayar da abinci ne a layin Itam da ke Garin Uyo.

Asirinta ya tonu ne bayan da wanda take zuwa wurinsa tana sayen ruwan da ya yi wa gawa wanka a dakunan da ake ajiye gawarwaki na kudi ya ce yana bin ta bashin kudi da ta sayi ruwan tsawon wata uku ba ta biya shi ba.

Ya ci gaba da cewa, a kullum sai ta zo wurinsa sayen ruwan sau biyu zuwa uku a rana.

Bangaren ’yan sanda kuwa sun ce a binciken da suka yi mata, ta tabbatar musu da cewa da gaske ne tana sana’ar sayar da abinci kuma da ruwan da aka yi wa gawa wanka take amfani domin duk wanda ya ci abincinta babu inda zai kara tafiya ya ci abinci sai ya dawo wurinta kuma tana samun kudi sosai.

An mayar da matar zuwa babban ofishin ’yan sanda da ke Uyo ana ci gaba da yi mata tambayoyi.