✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama Dan NYSC kan aikata fyade

An cafke wani mai yi wa kasa hidima bisa zargin yi wa kawar budurwarsa fyade a cikin makarantar da yake koyarwa a wani kauye a…

An cafke wani mai yi wa kasa hidima bisa zargin yi wa kawar budurwarsa fyade a cikin makarantar da yake koyarwa a wani kauye a jihar Ogun.

Kakakin ‘yan sandan jihar, ya ce an tsare tsare mai yi wa kasa hidiman ne bayan da yarinyar ta kai kara caji ofis cewa ya yi mata fyade.

Ya ce yarinyar, mai shekara 20 da mai yi wa kasa hidiman ya yi wa fyade kawar budurwarsa ce daga kauyen aika-akAgbajege da ke Karamar Hukuamr Obafemi-Owode.

Ta sajoda wa ‘yan sanda cewa wanda ake zargin ya yi mata fyade ne a lokacin da ta raka shi domin yin sayayya.

Ta ce ya yaudare ta ne da cewa zai saya mata kyautar bikin zagayowar ranar haihuwarta, a matsayin saurayin budurwarsa, har ya bukaci ta raka shi..

A hanyar zuwa kasuwar ne ya nuna mata cewa ya manta lalitarsa a dakinsa da ke masaukin masu yi wa kasa hidima d ake harabar makarantar da yake koyarwa.

A cewarta, ko da ya nemi ta raka shi can ya dauko lalitarsa, ba ta kawo wani abu a ranta ba, kasacewar saurayin kawarta ne.

Amma zuwansu ke da wuya ya finciko ta ya shigar da ita dakin ya yi mata fyade, duk da kururuwa da rokon sa da ta yi.

Bayan ta kai kara ne PDO ya tura ‘yan sanda suka tiso keyar wanda ake zargin,  wanda a halin yanzu yake tsare ana gudanar da bincike.

Ya ce matashin ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya aikata, amma bai san abin da ya kai shi ba, budurwar kuma an kai ta Babban Asibiti na Owode Egba domin duba lafiyarta.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin domin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya.