✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai wa ofishin ’yan sanda hari a Anambra

Da safiyar Litinin ce wasu bata gari suka kai farmaki ofishin rundunar ’yan sanda da ke yankin Ukpo a Karamar Hukumar Dunukofia ta Jihar Anambra.…

Da safiyar Litinin ce wasu bata gari suka kai farmaki ofishin rundunar ’yan sanda da ke yankin Ukpo a Karamar Hukumar Dunukofia ta Jihar Anambra.

Ya zuwa yanzu babu wani takamaiman bayani kan aukuwar hari, amma wani bidiyo da wani jami’in dan sanda a shelkwatar ya dauka ya nuna wani bangare na ofishin rundunar na ci da wuta.

Wata majiya da ta tabbatar da faruwar lamarin da ya auku a kan hanyar Enugu zuwa Onitsa, ta ce masu ababen hawa sun rika tseren barin wurin gudun kar harin ya ritsa da su.

Ya zuwa wannan lokaci, wakilinmu, ya kasa samun kakakin ‘yan sandan jihar Misis Nkeiruka Nwode.

A makon jiya ne wasu ’yan bindiga suka kai hari ofishin ’yan sanda da ke Ekori a Karamar Hukumar Yakurr ta Jihar Kuros Riba inda suka kwashi bindigu.