✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai wa Firaministan Japan hari yana tsakar yakin neman zabe

Wani jami’in dan sanda daya ya jikkata.

An jefi Firaministan Japan Fumio Kishida da konson bam mai hayaki yayin da yake dab da gabatar da jawabi a wajen wani taron yakin neman zabe.

Bayanai sun ce an kai wa Firaminstan hari ne a garin Wakayama da ke gabashin Japan a wannan Asabar din.

Firaministan dai ya tsallake rijiya da baya babu ko kwarzane yayin da jami’an tsaron suka gaggauta ficewa da firaministan daga zauren taron.

Sai dai wani jami’in dan sanda daya ya jikkata a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.

Tuni dai ’yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi bayan aukuwar lamarin.

A watan Yulin bara ma haka aka harbi tsohon Firaministan kasar, Shinzo Abe inda ya sami mummunan rauni a lokacin da yake gabatar da jawabi a birnin Nara.