✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An jibge ’yan sanda 5,000 domin zaben kananan hukumomin Ondo

Rundunar ’Yan Sandan ta Jihar Ondo ta tanadi ma’aikata 5,000 da za su samar da tsaro a zaben kananan hukumomin jihar da za a gudanar…

Rundunar ’Yan Sandan ta Jihar Ondo ta tanadi ma’aikata 5,000 da za su samar da tsaro a zaben kananan hukumomin jihar da za a gudanar a ranar Asabar 22 ga watan Agusta.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Bolaji Salami, a zantawarsa da ’yan jarida, ya ba da tabbacin isassun matakan tsaro da aka daukar wa zaben.

Ya ce ’yan sandan za su yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro da suka hadar da ma’aikatan Hukumar Tsaron Cikin Gida (NSCDC) da kuma Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).

Kwamishinan ya yi kashedi ga masu neman tayar da zaune tsaye gabani da kuma bayan zabe, tare da kira ga masu ruwa da tsaki na siyasa a jihar da su kiyaye ka’idodin zaben.

Ya ce suna kuma shirin tanadar wasu karin jami’ai gabanin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 10 ga watan Oktoba, inda ya jaddada tsayuwar dakan da ya yi a kan tabbatar da zaben ya gudana cikin lumana.

Mista Salami ya ce za a debo karin ’yan Sanda daga jihohi masu makwabtaka da suka hadar da Osun, Ogun da kuma Ekiti doriya a kan ’yan sanda 5,000 da aka tanada tun a yanzu.

Domin tabbatar da tsaro yayin zaben, Kwamishinan ya ce za a jibge akalla ’yan sanda 10 da za su sanya ido a kowace rumfar zabe.