✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An harbe alkali a cikin kotunsa a Imo

Maharan sun isa kotun ne a kan babura

Wasu ’yan bindiga a ranar Alhamis sun harbe wani alkalin kotun majistare, Nnaemeka Ugboma, a Jihar Imo.

Kafin a kashe shi, marigayin shi ne ke jagorantar kotun majistare da ke Ejemekwuru a Karamar Hukumar Oguta ta Jihar ta Imo.

Aminiya ta gano cewa maharan sun yi wa kotun tsinke ne a kan babura, sannan suka fito da alkalin da karfin tsiya, suka harbe shi a ka.

Kazalika, maharan sun yi ta harbi a sararin samaniya don su tsorata mutanen da suke harabar kotun a lokacin, bayan aikata kisan.

Marigayi alkalin dai dan asalin yankin Nnebukwu ne da ke Karamar Hukumar ta Oguta.

Babu dai wanda ya san asalin musabbabin kisan, amma wakilinmu ya ce mutane sun rika guduwa suna barin gidajensu a lokacin harin.

Wani abokin aikin mamacin, Emperor Iwuala, ya tabbatar da kisan a cikin wata gajeruwar sanarwa.

Shi ma Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Owerri, Ugochukwu Allinor, ya tabbatar da kisan.

To sai dai har yanzu Kakakin ’yan sandan Jihar, Henry Okoye, bai magantu ba a kan lamarin.