✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hana Ganduje shiga wurin manyan baki a filin rantsar da Tinubu

Shi ma gwamnan Anambra, Charles Soludo ya yi kokarin shiga amma jami’an tsaro suka taka masa birki.

Gwamnan Jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje ya gamu da cikas a bikin rantsar da sabon Shugaban Kasa a Eagle Square da ke Abuja.

Ganduje da matarsa Hafsat sun yi kokarin shiga cikin wurin da ake kebe wa manyan baki masu alfarma amma sai jami’an tsaro suka dakatar da shi.

Jami’an tsaron sun yi wa Ganduje bayanin cewa takardar gayyatar da yake da ita koriya ce kuma sai mai takardar gayyata mai ruwan gwal ne zai shiga cikin wannan bangaren.

BBC ya ruwaito cewa Ganduje ya jira na tsawon fiye da minti 10 kafin ya dauki kaddara ya koma bangaren da aka tanadar wa baki irinsa.

Shi ma gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludoya yi kokarin shiga wannan bangaren amma kamar Ganduje shi ma jami’an tsaro sun taka masa birki.