✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano badaƙalar biza ta N500m da kama mutum huɗu a Legas

An tabbatar da kamen tare da bayyana cewa, badaƙalar ta shafi sama da mutane 100 da aka damfara da kuma jimillar kuɗi sama da Naira…

Jami’an rundunar ’yan sandan Jihar Legas sun gano wata badaƙalar biza ta miliyoyin Naira tare da cafke wasu mutane huɗu da ake zargi da hannu wajen damfarar mutane sama da 100 fiye da Naira miliyan 500.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da Blessing Wefsutu mai shekara 27 da Chineye Christian, mai shekara 36 sai Archbong Udeme Ifereke, mai shekara 23; da Maurine Peter, mai shekara 25, dukkansu ma’aikatan wani Kamfanin tuntuɓa ne na ilimi da ke unguwar Ago Okota a Legas.

Tun da farko an kai rahoton lamarin a ofishin ’yan sanda na Ago Okota kafin daga bisani a miƙa shi zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar da ke Yaba domin gudanar da bincike mai zurfi.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, kamfanin tuntuɓa da ke fakewa da bayar da izinin gudanar da bizar aiki na Kanada da Ostireliya, ana zarginsa da karɓar maƙudan kuɗaɗe daga hannun waɗanda abin ya shafa. Rahotanni sun nuna cewa, waɗanda ake zargin sun yi alƙawarin ba su damammakin yin aiki a ƙasashen waje amma sun kasa cika alƙawurran da suka ɗauka, lamarin da ya kai ga shakku, daga bisani ’yan sanda suka shiga lamarin.

Kakakin rundunar ’yan sandan, Benjamin Hundeyin, a wata sanarwa da ya fitar ta hanyar dandalin sada zumunta na X a ranar Laraba, ya tabbatar da kamen tare da bayyana cewa, badaƙalar ta shafi sama da mutane 100 da aka damfara da kuma jimillar kuɗi sama da Naira miliyan 500.

“Bincike na ƙara nuna cewa ƙungiyar ta haɗa da ƙarin da ke da hannu  waɗanda a halin yanzu ke hannu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Rundunar ta na ƙara ƙaimi wajen cafke waɗanda ake zargi da shirin gudu tare da tabbatar da gurfanar da duk waɗanda ke da hannu a gaban shari’a.”

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas, CP Olohundare Jimoh, ya buƙaci mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan tare da tabbatar da sahihancin hukumomin don tafiye-tafiye da ɗaukar ma’aikata kafin su shiga duk wata hulɗa da ta shafi biza.

Ya jaddada ƙudirin rundunar na kare al’umma daga makircin damfara da kuma tabbatar da cewa, masu aikata laifin sun fuskanci cikakken hukunci da dokar ƙasa ta tanada.