✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fitar da Ronaldo daga Gasar Kofin Saudiyya

Ronaldo ya yi ta kai farmaki tare da baras da damarmaki da dama na cin kwallo.

Cristiano Ronaldo ya fusata bayan da Al-Wehda ta yi waje da kungiyarsa ta Al-Nassr daga Gasar Cin Kofin Saudiyya.

Wannan na zuwa ne bayan da suka doke abokan karawarsu da ci 4-0 watanni biyu da suka gabata a gasar lig na Saudiya.

A wancan wasan da wanda Al-Nassr ta yi bushasha, Ronaldo ya ci dukkan kwallaye hudu, lamarin da ya sa aka yi tsammanin kungiyar masu masaukin bakin ta Al-Wehda ba za su kai ga wasan karshe don karawa mai zafi da Al-Hilal ba, sai ga shi an yi waje da su.

Dama kwallo daya kacal Wehda ke nema don hayewa zuwa wasan karshe, wajen fitar da Al-Nassr ta Ronaldo daga gasar a matakin wasan kusa da na karshe.

Ronaldo ya yi ta kai farmaki tare da baras da damarmaki da dama na cin kwallo, a fafatawar da suka karkare da ’yan wasa goma saboda jan kati da Abdullah Al-Hafith ya samu.