✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara raba wa asibitocin Kano kayan tallafin COVID-19

Kimanin asibitoci 175 ne aja raba wa kayan

Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano tare da hadin gwiwar Hukumar Tattarawa da Adana Magunguna ta Jihar sun fara rabon kayan tallafin Kwarona na CACOVID ga asibitoci 175 da ke fadin jihar.

Asibitocin sha-ka-tafi 131 da kuma manyan asibitoci na kananan hukumomi 44 ne za su ci gajiyar rabon kayan tallafin.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da rabon kayan, Shugaban hukumar, Hisham Imamuddeen, ya ce yunkurin na daga cikin kudurin Gwamnatin Jihar na inganta lafiyar al’umma.

Ya ce, “Asibitoci suna da bukatar kayan aiki domin ci gaba da kula da lafiyar al’umma musamman a wannan lokaci da yawan mutane ke karuwa.

“Wadannan kaya za mu raba su ne ga wadanda aka kwashe daga cibiyar killace masu cutar COVID-19 da ke filin wasa na Sani Abacha a Kofar Mata a Kano, sakamakon barkewar annobar,” inji shi.

A nata bangaren, Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Lafiya ta jihar, Amina A. Musa, ta yi kira ga asibitocin da suka ci gajiyar rabon da su yi amfani da su yadda ya kamata.

“Sanin kowa ne mun samu wannan tallafi a lokacin da muke tsaka da yaki da annobar COVID-19 daga wajen wasu masu kishin al’umma irin u Dangote da BUA, wadanda suka tallafa wajen inganta wuraren ajiyar wadanda suka kamu da annobar,” inji ta.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar rabon kayan sun yaba wa kokarin gwamnati tare da alkawarin yin amfani da su ta hanyar da ta dace.