✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dawo da ’yan Najeriya 104 da suka makale a Chadi —NEMA

Hukumar ta ce za ta horar da su sana'o'i don su dogara da kansu.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta ce ta karbi ’yan Najeriya 104 da suka makale a kasar Chadi a hanyarsu ta zuwa kasashen Turai neman aiki ta barauniyar hanya.

Da yake karbar su a Filin Jirgi na Malam Aminu Kano ranar Talata, Kodinetan NEMA a Jihar Kano, Nuradeen Abdullahi, ya ce mutanen sun hada da maza 34 da mata 18 da yara 52 daga jihoihn Kano da Katsina da Borno da Akwa Ibom da kuma Yobe.

Abdullahi wanda shugaban ma’aikatan NEMA a Kano, Suleiman Sa’ad-Abubakar, ya wakilta, ya ce an kwaso ’yan Najeriyan ne “bisa kulawar Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) daga N’Djamena, babban birnin kasar Chadi karkashin shirin mayar da su gida a son ransu.

“An samar da shirin ne ga marasa galihu da suka bar kasarsu don neman abun duniya a kasashen Turai kuma suka kasa komawa gida,” in ji shi.

A cewarsa, gwamnati za ta koya musu sana’o’in dogaro da kai sannan ya bukace su da su kasance masu bin doka da oda.

Abdullahi ya shawarci ’yan Najeriya su guji yin hijira ba bisa ka’ida ba, wanda ke jefa rayuwarsu cikin hadari ta hanyar tafiye-tafiyen neman abun duniya a wasu kasashe.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa hukumar ta karbi ’yan Najeriya 444 da suka makale daga Yamai na kasar a Jamhuriyar Nijar tsakanin watan Fabrairu zuwa Afrilu, 2023.