✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An damke wasu mata biyu kan zargin satar yarinya a Oyo

An damke wasu mata biyu tare da gurfanar da su a kotun majistare da ke Ibadan, babban birnin jihar bisa zargin sace wata yarinya mai…

An damke wasu mata biyu tare da gurfanar da su a kotun majistare da ke Ibadan, babban birnin jihar bisa zargin sace wata yarinya mai shekara biyu.

Bayanan da kotu ta samu sun nuna wadanda ake zargin sun aikata laifin da ake tuhumarsu ne a watan Yulin 2022 da ya gabata.

An ce sun sace yarinyar ne a wajen iyayenta a yankin Akanbi da ke Ibadan a jihar.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeta Folake Ewe, ta shaida wa kotun cewa masu kare kansu tare da wasu da ake nema ruwa a jallo, sun hada baki wajen sace yarinyar.

Ta kara da cewa, ana tuhumar matan ne kan aikata sata da hada baki wajen aikata laifi, wanda a cewarta hakan ya saba wa sassa na 516 da 371 Kundin Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Oyo na shekara ta 2000.

Sai dai wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin da ake zarginsu da shi.

Alkalin kotun, Misis Patricia Adetuyibi, ta ba da belin matan a kan N100,000 ga kowacce, tare da shaidu bibbiyu.

Sannan ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 12 ga Janairun badi.

(NAN)