✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da ’yar tseren Najeriya saboda amfani da haramtattun kwayoyi

Nwokocha ta lashe lambar zinare a tseren da ta doke abokan karawarta na Ingila da Jamaica. 

Hukumar kula da ’yan wasan tsalle-tsalle ta sanar da dakatar da ’yar wasan tseren, Nzubechi Grace Nwokocha, saboda zargin amfani da haramtattun kwayoyi.

Cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, Athletics Integrity Unit (AIU) ta ce dakatar da ’yar wasan mai shekara 21 bayan samun burbushin kwayoyin Ostarine da Ligandrol a cikin jinin Nwokocha bayan gwajin da aka yi mata.

“AIU ta dakatar da ’yar tseren Najeriya Nzubechi Grace Nwokocha saboda amfani ko kuma samun kwayoyin da aka hana amfani da su a jikinta (Ostarine da Ligandrol),” a cewar AIU.

Hakan na nufin ba za ta sake shiga wasanni ba har sai an yanke hukuncin karshe yayin zaman da za a yi karkashin jagoranci da dokokin Hukumar Hana Zamba a wasanni ta WADA.

Ana fargabar akwai yiwuwar a kwace kyautar zinariyar da Najeriya ta samu a tseren.

Nzubechi Grace Nwokocha da sauran ‘yan tseren Najeriya
Nzubechi Grace Nwokocha a filin daga

Nwokocha tana cikin tawagar ’yan mata hudu – Tobi Amusan da Favour Ofili da Rose Chukwuma – wadanda suka lashe lambar zinare a gasar kasashen rainon Ingila ta 2022 a wasan tsere na tsallake shinge.

A watan da ya gabata ne Nwokocha ta lashe lambar zinare a tseren da ta doke abokan karawarta na Ingila da Jamaica.