✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto mutum 13 da ake shirin safarar su zuwa Libya a Kano

Hukumar nan mai Yaki da Safarar Mutane a Najeriya (NAPTIP), ta sanar da samun nasarar ceto wasu ’yan kasar 13 a Jihar Kano da aka…

Hukumar nan mai Yaki da Safarar Mutane a Najeriya (NAPTIP), ta sanar da samun nasarar ceto wasu ’yan kasar 13 a Jihar Kano da aka yi yunkurin safarar su zuwa kasar Libiya.

Jami’in Hulda da Al’umma na Hukumar a reshenta na Kano, Aliyu Abba Kalli ne ya shaida hakan ga sashen Hausa na BBC.

A cewarsa, NAPTIP ta samu nasarar ceto mutanen ne bayan samun bayanan sirri daga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya wato DSS.

Ya ce DSS ta ankarar da su dangane da bayanan da ta samu na ajiye mutanen da aka yi a wani gida da ke birnin Bandirawo da nufin ketarewa da su ta cikin Nijar zuwa Libiya.

Bayanai sun ce, daga cikin mutanen da aka ceto akwai mata 11 da maza biyu, wadanda shekarunsu suka kama daga 15 zuwa 35.

“Mun samu nasarar ceto mutanen ne bayan samun bayanan sirri daga Hukumar Tsaro ta DSS.

“Bayanan sirrin sun nuna cewa an debe yara daga Kudanci zuwa Arewacin Najeriya za a fitar da su zuwa Libya.

“Duk mafi yawanci kabilar Yarbawa ne.

“Mun same ne a nan Bandirawo suna hanyarsu ta zuwa Daura kuma muna da yakinin cewa za su bi ta hanyar Kwangwalam.

“A halin yanzu duk suna hannu, kuma wanda muke zargin ya dauko su shi ma yana hannu.

“Za mu ci gaba da gudanar da bincike, a cewar Kalli.

Kalli ya ce ko a watan da ya gabata ne sun samu nasarar ceto wasu yara 52 a Jihohin Kano da Jigawa bayan samun bayanan sirri daga Ofishin Mai ba da Shawara kan Harkokin Tsaro na Kasa.