✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke matar da ta jima tana buga jabun kudi a Ogun

An cafke matar dauke da jabun kudi har N24,000 a jakarta.

Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta cafke wata mata mai shekara 30 da ake zargi da kashe jabun kudi na Naira dubu daya a kasuwar Kila da ke Karamar Hukumar Odeda a Jihar.

Kakakin rundunar a Jihar, Abimbola Oyeyemi ne, ya tabbatar wa maneman labarai hakan a Abeokuta ranar Jumaa.

Ya ce, “Bayan gudanar da bincike, mun gano jabun kudi har N24,000 a cikin jakarta.

“Bayan tuhumarta, ta bayyana cewar ta na hada jabun kudi da masu kyau sai ta shiga kasuwa ta yi sayayya,” a cewar Oyeyemi.

Kakakin ya kuma ce bayan samun rahoton da jami’an ’yan sandan Jihar suka yi, sun shiga bincike yayin da daga karshe suka yi nasarar cafke ta.

Kazalika, kakakin ya ce bincikensu ya gano jami’an tsaro sun kama matar a lokuta daban-daban kan laifin amfani da jabun kudi a kasuwannin Abeokuta.

Abimbola ya kuma ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Lanre Bankole, ya ba da umarnin mayar da ita Sashen Binciken Manyan Laifuffuka, don fadada bincike.