✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke dan aikin shugaban kungiyar ISWAP

An cafke Wida Kachalla da mai jigilar kayan kungiyar ISWAP a kasuwa.

Sojoji sun cafke dan aiken kwamandan kungiyar ISWAP, Modu Sulum, tare da mai yi wa kungiyar safarar kayan masarufi.

Kafar yada labarai ta PRNigeria ta ce an kama Wida Kachalla, wanda dan daki ne ga Modu Sulum, wanda sojojin rundunar Operation Hadin Kai suka kashe a Jihar Borno.

Sojojin, karkashin jagorancin Manjo DY Chiwar sun ritsa Wida Kachalla tare da mai safarar kayan masarufin kungiyar ne a kasuwar garin Benisheik a Jihar ta Borno.

Ritsa ’yan ISWAP din da sojojin suka yi ke da wuya, sai Wida Kachalla ya tattauna layukan wayarsa ya hadiye domin ya salwantar da wasu muhimman bayanan da sojoji za su iya samu daga wayarsa.

PRNigeria ta ruwaito wata majiyar tsaro na cewa, “A ’yan makonnin nan mun katse layin sadarwar ’yan ta’adda da hanyoyinsu na jigilar kayan bukatarsu.

“Wanda ake zargin ya cinye layukan wayoyinsa ya hadiye, amma duk da haka mun samu muhimman bayanai.”