✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke basarake a cikin ’yan bindiga a Neja

Mai Garin na cikin ’yan bindiga 11 da suka gwabza kazamin fada da jami'an tsaro

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta cafke Mai Garin Tungan-Iliya da wasu mutum 10 bisa zargin aikata ta’addanci a Karamar Hukumar Mashegu da ke jihar.

Kakakin rundunar, ASP Wasiu Abiodun ya ya ce bayan samun rahoto a ranar 25 ga watan Disamba 2020, sun kai samame maboyar ’yan bindigar da ke dajin Tungan-Iliya.

“Jami’anmu sun yi dauki ba dadi da ’yan bindigar kuma an cafke mutum 11 daga cikinsu, sai guda biyar da suka ji raunuka.

“Daga cikin wanda aka kama akwai Mai Garin kauyen Tungan-Iliya da kuma wata mace da ke kai wa ’yan bindigar rahoto,” cewar Abiodun.

Ya kara da cewa rundunar na ci gaba da bincike, da kuma da zarar ta kammala za ta mika wadanda ake zargin zuwa kotu.

Har wa yau, ya ce a ranar 25 ga Disamba, rundunar ta samu bayanan sirri cewar, ’yan bindiga sun farmaki yankin Gambo da ke Karamar Hukumar Rafi, inda suka yi garkuwa da mutum hudu.

Daya daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su, an ceto shi, ragowar kuma ana ci gaba da kokarin kubutar da su tare da cafke masu garkuwar.