✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ya kamata gwamnatin Katsina ta bude layukan sadarwa’

Kungiyoyin sun bukaci gwamnatin Jihar ta yi koyi da Kaduna da Zamfara.

Gamayyar kungiyoyin farar hula ta Karamar Hukumar Funtua da ke Jihar Katsina, ta yi kira ga gwamnatin Jihar da ta bude hanyoyin sadarwa a dukkan sassan Jihar da aka katse tsawon lokaci.

Wannan kiran na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban gamayyar kungiyoyin Alhaji Umar Imama da sakatarensa Rabiu Umar Maska, wacce suka fitar ranar Alhamis a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa kungiyoyin sun yi kira ga Jihar da ta yi da makwabtanta na Kaduna da Zamfara wajen dawo da hanyoyin sadarwar.

“Hakan zai rage radadin wahalar da mutane ke ciki a yanzu. Sannan dokar hana zirga-zirga, idan tana haifar da sakamakon da ake so, yana da kyau a kara lokaci zuwa karfe 10 na dare.

“Wannan shi ne lokacin da kusan daukacin mutane ke kammala harkokin kasuwancinsu na yau da kullum.

“Sannan a dakatar da irin cin zarafi da ’yan sanda ke yi wa al’umma masu amfani da babura,” a cewar sanarwar.

Har wa yau, gamayyar kungiyoyin ta bukaci Gwamnatin Jihar da ta samar da kayan tallafi ga mabukata, don rage radadin halin da suke ciki.

“Yana da kyau a tallafa wa matasa musamman wanda suka rasa ayyukansu ko kasuwancinsu. Hakan zai hana su shiga aikata miyagun laifuka.

“Yana da kyau Gwamnati ta ci gaba da kyautata tsarin hadin kan jami’an tsaro da al’ummar yankuna don samar da abin da ya dace,” inji gamayyar kungiyoyin.