✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An binne gawar Sarauniya Elizabeth II

An binne gawar Sarauniyar kwanaki 11 bayan rasuwarta.

An binne gawar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II a Windsor Castle, kwanaki 11 bayan rasuwarta.

A Yammacin Litinin ne dai aka gudanar da jana’izar kasar ga Sarauniyar, wadda shugabannin kasashen duniya daban-daban suka halarta.

Iyalan gidan sarautar da dama ne suka shiga tattakin raka akwatin gawar zuwa cocin St George, kafin a binne ta.

Sarki Charles na III, Gimbiya Anne, Yarima Andrew da Edward, da kuma Yarima William da Harry na cikin tawagar da suka yi wa gawar rakiya.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, an fara saka gawar Sarauniyar ce a cikin taskar adana gawa a cikin cocin na St George, gabanin yi mata jana’izar karshe da iyalan gidanta suka yi mata.

Akwatin gawar Sarauniya Elizabeth II

Sarki Edward IV ne aka fara binnewa a cocin na Fadar Windsor, wanda ya kasance a karkashin ikon gidan Sarautar na kusan shekara 1,000.

Tsoffin Sarakuna da yawa aka binne a cocin, wadanda suka hada da Sarki George IV da George III, wanda a zamanin mulkinsa ne Amurka ta samu ’yancin kai daga daular Birtaniya.

Sarakuna da dama ne dai aka binne tare da taskancewa a wurare daban-daban cikin cocin

An binne Sarauniyar a kusa da kabarin mijinta Duke na Edinburg, Yarima Philip, a cocin inda a nan ne aka binne mahaifinta Sarki George VI da mahaifiyarta da kuma kanwarta gimbiya Margaret.

Fiye da manyan baki 2000 ne suka halarci janazar Sarauniyar wadda ta riga mu gidan gaskiya a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumba bayan shafe shekaru 96 a ban kasa.