✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ba hammata iska tsakanin mabiya addinin Hindu da Musulmai a Indiya

Rikicin ya faru ne a birnin New Delhi, yayin muzaharar mabiya addinin Hindu

Wani rikici ya barke yayin wata muzaharar mabiya addinin Hindu a New Delhi, babban birnin kasar Indiya ranar Asabar, inda mutane da dama suka jikkata, cikinsu har da ’yan sanda.

Rikicin ya faru ne tsakanin Musulmai da mabiya addinin Hindun a yankin Jahangirpuri, da ke wajen birnin na Delhi, kamar yadda wani ganau ya tabbatar.

’Yan sanda dai sun ce har yanzu suna ci gaba da binciken musabbabin ba hammata iskar.

“Har yanzu muna kan bincike don gano yawan mutanen da suka jikkata…an ji wa wasu ’yan sanda ma rauni,” inji Deependra Pathak, wani jami’in dan sanda a Jahangirpuri.

’Yan sanda sun ce rikicin dai ya barke ne yayin muzaharar da mabiya Hindun ke yi don bikin Hanuman Jayanti, ko da yake ba su yi karin haske a kai ba.

Tun gabanin rikicin dai, wasu masu zanga-zanga a birnin na New Delhi sun rika rera wakokin kin jinin gwamnatin Firaministan kasar, Narendra Modi.

Suna dai zargin hukumomin kasar ne da kai wa Musulmai hari da gangan, bayan wata taho-mu-gamar da aka samu a makon da ya gabata a Jihohi ukun da jam’iyyar Firaministan ke mulki.

Rikicin makon jiyan dai ya tilasta wa ’yan sanda kakaba dokar hana fita a wani gari, tare da hana taruwar sama da mutum hudu a wasu sassan Jihohin.

’Yan adawa a Indiya dai na zargin jam’iyyar Firaminista Modi mai ra’ayin rikau da rura wutar rikici tsakanin mabiya addinan biyu a Jihohin da take mulki.