✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An aika ’yan bindiga da dama lahira a Zamfara

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga da ba a tantance adadinsu ba a Zamfara.

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga da dama a Jihar lokacin da suka yi yunkurin kai hari a kauyen Magami da ke Karamar Hukumar Gusau.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Zamfara ta sanar da haka ne ta hannun jami’in hulda da jama’anta, SP Shehu Mohammed, a Gusau.

“Rundunar ta samu rahoto cewa ’yan bindiga  masu yawa sun mamaye garin Magami na Karamar Hukumar Gusau da niyyar afka wa al’ummar garin a daren Asabar.

“Kwamishinan ’yan sanda, Hussaini Rabiu, ya umarci rundunonin ‘PMF/CTU/Special Forces’ da kuma ‘Operation Puff Adder’ da ke yankin da su hada karfi da karfe don tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Rundunonin sun bazama cikin kwarin gwiwa suka kai dauki inda suka yi musayar wuta da maharan.

“Sakamakon artabun, an samu nasarar dakile harin, yayin da aka kashe ’yan bindiga  da ba a tantance adadinsu ba, da yawa daga cikinsu kuma suka tsere da raunukan harbin bindiga,” inji Shehu.

Sai dai ya ce: “Jami’anmu biyu sun rasa rayukansu yayin kare al’ummar, amma babu wani farar hula da ya rasa ransa.”

Ya kuma bayyana cewa Kwamishinan ya tura karin jami’an tsaro zuwa yankin domin su ci gaba da kare yankin da nufin magance sauran hare-hare a kauyukan da ke kusa.

Kwamishinan ya sake nanata gargadinsa ga duk ’yan bindiga a jihar da su mika makamansu su rungumi zaman lafiya ko kuma su fuskanci sakamakon ayyukansu.