✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka za ta tallafa da Dala miliyan 45.5 don gyaran Arewa maso Gabas

Gwamnatin Amurka ta ce za ta bayar da karin tallafin Dala miliyan 45 da dubu 500 (kimanin Naira biliyan 16 da miliyan 380) kan aikin…

Gwamnatin Amurka ta ce za ta bayar da karin tallafin Dala miliyan 45 da dubu 500 (kimanin Naira biliyan 16 da miliyan 380) kan aikin sake gyara Arewa maso Gabas. Mataimakin Sakataren Harkokin Cikin Gidan Amurka, John Sulliban ne ya fadi haka a taron da Amurka da Najeriya suka yi a Abuja ranar 20 ga Nuwamba. Mista Sulliban ya ce tallafin zai taimaka wa wadanda rigingimu ya shafa a Arewa maso Gabas don sake gina rayuwarsu. “Ina farin cikin sanar da cewa Amurka ta hanyar abokan aikinmu a Hukumar USAID, za ta tallafa da karin Dala miliyan 45 da rabi don taimakawa wajen daidaitawa da kuma yunkurin gaggauta farfado da rayuwar jama’ar da rikici ya shafa a Arewa maso Gabas su sake gina rayuwarsu.”

Sai ya yi kira ga gwamnati ta ci gaba da bin dukan hanyoyin da suka dace domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma bukansa ci gaba a Arewa maso Gabas. Mista Sulliban ya yi kiran a samu karin hadin kai tsakanin gwamnatin da kungiyoyin jama’a da shugabannin al’umma don samar da ingantattun “kayayyakin jin dadin rayuwa da tattalin arziki da siyasa da za su taimaka wajen samar da zaman lafiya mai dorewa da kuma ci gaba.” Ya ce wadannan abubuwa wajibi ne su hada da “gudanar da bincike na gaskiya kan take hakkin dan Adam da hanyoyin da za a hukunta wadanda aka samu da laifi. Hakan yana da muhimmanci wajen karfafa yarda jama’a ga gwamnati da karfafa zaman lafiya a Arewa maso Gabas da inganta hadin gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya.