✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta haramta kayan China kan musguna wa Musulmi

Shugaban Amurka Donald Trump ya haramta shigar da kaya kasarsa daga yankin Xinanjing na kasar China saboda gallaza wa Musulmi da ake yi a yankin.…

Shugaban Amurka Donald Trump ya haramta shigar da kaya kasarsa daga yankin Xinanjing na kasar China saboda gallaza wa Musulmi da ake yi a yankin.

Amurka ta hana shigowar kayan kanfanonin yankin Xianjiang inda Gwamnati China ke musguna wa Muslumi ’yan kabilar Uighur ne a matsayin karin matsin lamba ga gwamnatin ta Chinar.

“Gwamnatin China na cin zarafin ’yan kabilar Uighur…tursasa wa mutane yin aikin karbi babban cin zarfi ne da tauye hakkin dan Adam”, inji Amurka.

Kwamishinan hukumar kare iyakoki da yaki da fasakwauri ta Amurka Mark Morgan, ya ce matakin na Shugaban Trump sako ne ga kasashen duniya cewa Amurka ba za ta lamunci bautar da al’umma ba.

Amurka ta ce ana tursasa wa Musulmi a Xianjing yin aiki tamkar fursunoni a kamfanonin da masana’antun auduga da sutura da kayan hada komfuta da na tumatur da sauransu.

Majalisar Dinkin Duniya na zargin Gwamnatin China da tsarewa da kuma azabtar da kusan Musulmi miliyan daya ’yan kabilar Uighur da sunan dalilan tsaro.

Gwamnatin China ta sha musanta gallaza wa Musulman na Uighur da ta killace ce a wasu sansanoni da ta kira na sauya tunanin masu ta’addanci, tana kuma koya musu sana’a.

Wani babban jami’in hukumar tsaron cikin gida ta Amurka, Ken Cuccinelli ya ce, “Wannan salon batar da mutane ne na zamani.

“Ba cibiyar koyar da sana’o’i ba ce. Wuri ne na tattara wasu kabilu ko mabiya wasu addinai ana tilasta musu yin aikace-aikace cikin kuntatawa ba tare da wani ’yanci ba”, inji shi.

Chana na noma kashi ashirin na audugar da ake fitarwa a kasuwannin duniya, kuma yawancin audugar na fitowa ne daga yankin Xinjiang.