✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka na leken asiri ta manhajar Muslim Pro

Rundunar Sojin Amurka ta ce tana amfani da bayanan mutane daga manhajojin Musulunci

Rundunar Sojin Amurka ta sayi rumbun adana bayanan wasu manhajojin da Musulmai fiye da miliyan 100 a sassan duniya ke amfani da su.

Wani bincike da mujallar intanet ta Motherboard ta wallafa ranar Litinin ya gano Sashen Ayyuka na Musamman na rundunar ya sayi rumbunan ne kuma tana tattara bayanan daga kamfanoni daban-daban.

Mafi shahara daga cikin manhajojin ita ce ta kiran Sallah da karatun Alkur’ani mai suna Muslim Pro, wacce aka sauke ta a kan wayoyi da kwamfutoci fiye da sau miliyan 98.

Kazalika mujallar ta rawaito cewa sauran manhajojin da rundunar ta saya sun hada da shafukan hada ma’aurata na Musulmai.

Binciken ya gano cewa kamfanonin kan tattara bayanan masu amfani da manhajojin ne wajen tsara tallace-tallace ga amfani da su.

Rundunar Sojin Amurka ta tabbatar da labarin

Kwamandan Sojin Ruwa na Amurkan, Tim Hawkins ya ce, “Za mu yi amfani da bayanan ne wajen taimaka wa ayyukanmu na musamman a kasashen ketare.

“Amma za mu tabbatar da kiyaye dukkannin dokoki da ka’idojin kiyaye bayanan sirri na mutane kamar yadda dokokin suka tanadar.

Daya daga cikin kamfanonin da ke sayar da bayanan wuraren da masu amfani da manhajojinsu suke, X-Mode, ya ce a wata yana lura da na’urori miliyan 25 a Amurka.

X-Mode ya ce a wata daya yana kuma lura da na’urori miliyan 40 a wasu kasashen Turai, Latin, Asiya da yankin Pacific.

A bincikenta, Motherboard ta sauke manhajar hada manema aure Musulmai na Muslim Mingle a kan wayar Android don ta gano me ke faruwa.

Motherboard ta ce ta bankado yadda Muslim Mingle ke tura wa X-Mode cikakken bayanan masu amfani da ita da adireshin Wifi dinsu.

Binciken ya kuma gano sauran manhajoji da ke tura bayanan inda masu amfani da su suke sun hada har da manhajar Accupedo mai lissafa takun mutum, Global Storms mai hasashen yanayi da sauransu.

Dan Majalisar Dattawan Amurka, Sanata Ron Wyden ya shaida wa Motherboard cewa Z-Mode ta amsa cewa tana sayar da bayanan da ta tattara ga “kwastomominsu Sojin Amurka”.

Ba laifi muka yi ba —X-Mode

“X-Mode ta ba da izinin amfani da bayanan ta ga wasu kamfanonin fasaha da kan yi aiki da rundunonin soji.

“Aikinmu da su na kasa da kasa ne a bangarori uku: yaki da ta’addanci, samar da tsaro na internet da kuma hasashen wuraren da ke iya samun barazanar COVID-19″, inji X-Mode ga wa mujallar Motherboard.