A jiya ne hukumomin lafiya na duniya suka yi bikin zagayowar ranar kiyaye kiba ta duniya, kuma a bana maudu’in ya tabo har da kiyaye aukuwar kiba ga yara (tunda matsalar ba manya kadai ta shafa ba), inda aka yi magana a kan hanyoyin kare kiba a yaran da illolin tsangwamar yara masu kiba. Wannan ya zamo wajibi saboda kiyaye aukuwar cututtukan da kiba kan haifar tun a kuruciya, abin da ba zai haifar wa yaran da mai ido ba.
Bikin ya nuna cewa da dama yara masu kiba ba sa samun annashuwa ko shiga cikin yara ’yan uwansu, domin wasanni na motsa-jiki saboda tsangwama da tsokana irin na yara, inda za a ji ana sa wa yara masu kiba sunaye iri-iri. To saboda wannan tsokana da dama yara masu kiba ba su son wasa cikin abokai sai dai zama a gida turus. Don haka ne idan ana so a kiyaye irin wannan tun farko kada ma a bar yaran su yi kiba. Wadansu da dama suna kibar ce saboda gado ba wai saboda suna cin abincin da ya fi karfinsu ba ne, wadansu kalilan dinsu kuma suna da kibar ce saboda yawan ci. To a masu yawan ci din dole sai ana yi ana taka musu birki a kan yawan cimakar, ana bambance musu abinci mai amfani da wanda zai iya sa su yi kiba. Su kuma masu kibar irin ta gado, ban da sassaita cimaka, sai ana yi ana karfafa musu gwiwa wajen shiga wasannin motsa-jikin da suke sha’awa, kada su rika kwanciya kawai a gida suna latsa waya ko na’urar wasa ta gem.
Wadanne cututtuka akan iya dauka idan aka hada bayan-gida da wani mai wata matsala?
Daga Maman Walida
Kamar yadda muka taba fada, in dai ana tsabtace bayan-gida yadda ya kamata, duk bayan amfani da aka yi da shi, ba yadda za a yi a kwashi cuta daga wani zuwa wata. Domin idan ba a tsabtace bayin ko ke kanki za ki iya sa wa kanki wasu cututtuka. Yadda abin yake shi ne, ku mata kusan a bude kuke, idan wani ruwa ya fallatso daga cikin bayi mai kwayoyin cuta ko da ke kika yi amfani da shi, in dai ya shiga hanyar mafitsara to zai iya kawo ciwon mafitsara a rika jin saurin fitsari da ciwon mara, wani lokaci ma har kwayoyin su hau koda su rika kawo ciwon kwibin baya da yunkurin amai. To wannan daga kwayoyin cuta na bayan gida kadai za a iya samu.