✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi daban-daban kan kiwon lafiya

Ni ma’aikacin lafiya ne a karamin asibiti na PHC wato sha-ka-tafi. To na taba yin allurar kiyaye kamuwa da cutar hanta ta Hepatitis B har…

Ni ma’aikacin lafiya ne a karamin asibiti na PHC wato sha-ka-tafi. To na taba yin allurar kiyaye kamuwa da cutar hanta ta Hepatitis B har sau uku, sai dai ba a jere ba, ina yi ina yin tafiya har dai abu ya ruguje. To yanzu na auna jinina don gwajin ciwon an ce babu. Ko shin zan iya sakewa tun da sau ukun da aka ce an fi so a yi su a jere?

Daga Iro Auwal Muhammad, Maiduguri

Amsa: A’a ba sai ka sake ba. Ana kyautata zaton wadancan na baya da ka yi za su ba ka kariya koda ba a lokutan da aka zayyana ka yi su ba. Abin da yake da muhimmanci shi ne cewa ka samu an yi maka har guda ukun. To yanzu da ka tashi yin gwaji maimakon ka je a yi maka gwajin ciwon Hepatitis B (Hepatitis B antigen test HbsAg), kamata ya yi ka nema a yi maka gwajin kariyar ciwon, abin da muke kira “Hepatitis B antibody test, HbsAb” wato a gwada a ga ko alluran rigakafin sun yi aiki. Sai dai wannan gwaji yana da wahalar samu a wasu wurare, don ba kowane dakin bincike ne ke da kayan aikin yin sa ba.

 

Ni bayani nake so game da maganin harbin kunama. Na gode.

Daga Hassan Ibrahim Warji

Amsa: Eh, akwai maganin harbin kunama a likitance amma ba kasafai akan yi amfani da shi ba, kuma ba mu sani ba ko a asibitocinmu ana samar da su a yanzu, kamar yadda akan samar da na sarar maciji. Domin harbin kunama bai kai harbin maciji hadari ba, domin ba kowane harbi ne ake masa magani ba. Wato ba kamar sarar maciji ba, shi harbin kunama ko da an kai mutum asibiti sai an ga ya fara nuna alamun dafi ya shige shi ake bayarwa, sabanin sarar maciji.

 

Wata mata ce ta yi hadarin babur ta fadi ta buga kanta. Tun daga lokacin ta daina ji ta daina magana. Yanzu tsawon shekara takwas ke nan. Tana zuwa asibitin Bidda amma babu canji. Ko akwai wata shawara?

Daga M. U. Niger

Amsa: Eh, ga alama da ta samu hadarin, ta buga kanta daidai wuraren da ke kula da ji da furuci, wato nan tsagin kwakwalwa na saman kunne bangaren hagun da ake kira Broca’s area da Wernicke’s area. Koda a bangaren dama aka fadi, ciwon zai iya kasancewa a sashen hagu domin buguwa na iya cilla ainihin gundarin kwakwalwa daya sashen mai kallonsa.

Da ma dai ka san buguwa a kwakwalwa ba karamar matsala ba ce, tana sa irin wannan, wasu lokuta ma har da matsaloli na rashin iya motsi akan samu idan matsalar ta shafi wani bangare na kwakwalwa mai kula da motsa wani sashe na jiki. Kuma da ma ya kamata a ce ka san idan aka ji ciwo a kwakwalwa na buguwa irin wannan ko na bugun jini, kwakwalwar na dadewa kafin ta farfado, idan ma ta farfado din ke nan. Don haka ba maganin rana guda ake yi ba. Wasu dabaru ake yi wa masu irin wannan matsala da ake kira rehabilitation, wanda ya hada da magunguna da dama masu tsada da sake koyar da furuci da sake koyar da fahimtar magana da sauran ire-irensu. Wato dai ba abu ne mai sauki ba, kuma ba na jin a nan garinku akwai asibitin da aka inganta domin ya ba da irin wannan kulawa. Ai za ka ga idan irin wannan hadarin ya samu wadansu manya ko ’ya’yansu sai an kai ga fita da su kasashe irin su Jamus domin a ba su wannan rehabilitation na musamman.

 

Me ke sa wa idan na yi barci nakan farka inji kamar na shake, har da tari. Ko me ke sa haka?

Daga Umar Durum, Bauchi

Amsa: Yawanci shakewa ko kwarewa cikin dare daga abincin da mutum ya ci ne kafin kwanciya. Wato idan mutum ya ci abincin dare bai bari ya narke ba ya je ya kwanta, to abincin zai iya dawowa makoshi ya shiga hanyar numfashi a ji an kware ana tari. Don haka ne mukan ce dole ne a ci abinci awanni uku zuwa hudu kafin kwanciya. Misali idan mutum na kwanciya karfe 10 na dare to ana so a ce kafin karfe bakwai ya riga ya gama cin abincin dare, idan an makara a ce kafin takwas.

 

Ni kuma nakan ji ciwon kai da kasala idan na ci kowace irin shinkafa. Shin hakan matsalar lafiya ce?

Daga Usman Ahmed Naga

Amsa: Eh, akwai wadansu mutane kalilan da sukan samu matsalar borin jini idan suka ci shinkafa. Borin jini da akan samu daga abinci an fi samunsa a abinci irin su kifi, kwai da madara da ayaba, amma ba shinkafa ba. Duk da haka dai ana ba da labarin mutanen da sai bayan sun ci shinkafa jikinsu kan rikice. Watakila kana daya daga cikinsu. Masu samun borin jini ko wasu alamomi na matsala daga wani nau’i na abinci sai dai su guje shi idan suna so su zauna lafiya.

 

Shin kwarin da mukan ci a cikin wake ba su da illa ga lafiya tunda an dafa?

Daga Aminu Isyaku, Katsina

Amsa: Eh, to ba a ce akwai wata illa kai-tsaye ba, tunda ka ce an dafa. Kawai dai kamata ya yi a rika ajiyar waken inda kwari ba za su hau ba, kamar a sa a wani gwangwani ko roba da kwarin ba za su iya shiga ba. Ko kuma idan ma sun shiga a tsince kwarin kafin a dafa. Wadannan dabaru sun fi a kan a ce an sa maganin kwari a waken wanda zai iya illa ga wanda ya ci. Wato shi kwaro bai wa mutum illa ba, amma maganin da aka sa ya kashe shi ya yi wa mutum illa.

 

Akwai illa idan ina wanke bakina da ruwan alumun?

Daga Hafsat A. Bauchi

Amsa: To ba za a ce akwai illa ba, amma dai ba wani amfani. Ruwan alumun ba ruwa ne da akan wanke baki da shi ba. An riga an zayyana abubuwa da akan iya wanke baki da su. Idan ba a samu makilin ba akan samu ruwan mouthwash, wani ruwan makilin da akan iya kurkure baki da shi. Za kuma a iya sa ruwan dumi mai gishiri, ban da ruwan mouthwash. Amma ba wata majiya kwakkwara da ta tabbatar za a iya amfani da ruwan alumun wajen wake baki.

 

Idan ina gaban wani babba ana yi mini tambayoyi kamar na mukabala sai in ji bakina ya bushe ko digon miyau babu. Matsala ce wannan kuma ko akwai mafita?

Daga I B Batsari

Amsa: Wannan ba matsala ba ce, kusan kowa idan zai gabatar da wani abu gaban mutane da fari kafin ya goge zai samu fargaba, haka ma farkon neman aiki idan ana yi wa mutum mukabala ta tambayoyi, duk ana samu. Kawai dai ta wani ce ta fi ta wani, kamar yadda ka ce kai har miyau ne ke kafe maka. Alama ce ta fargaba da tsoro mai tsanani. Yadda za ka rage hakan shi ne ta hanyar rihasa, wato atisaye, ka rika gwaji kamar sau goma a gaban ’yan uwanka kafin ka je duk wata mukabala.