✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi daban-daban

A ’yan kwanakin nan ne na lura da wani dan kumburi a bayan hakarkarina. Ba ya yi mini wani ciwo. Na je asibiti likita ya ce…

A ’yan kwanakin nan ne na lura da wani dan kumburi a bayan hakarkarina. Ba ya yi mini wani ciwo. Na je asibiti likita ya ce kitse ne ya taru a wurin. To me yake kawo shi? Idan ba a cire ba akwai wata matsala?

Daga D.R.Z

 

Amsa: Eh, ga alama wani tsiro ne da mukan kira da lipoma wanda yake nufin tsiron kitse a karkashin fata. Yana nan za ka gan shi kamar babban kurji, amma mai taushi. Tsiron zai iya nuni da cewa mutum na da kitse da yawa a jiki ke nan wato wata alama ce ta cewa akwai kitsen da ya wuce kima a jikin mutum. Haka kawai yake fitowa ba dalili, ba kuma ya yin wani zogi ko zafi, shi ya sa wadansu ma ba sa lura da shi sai dai a gani a fada musu, kamar idan a gadon baya ne. Yana iya fitowa a ko’ina inda ake ajiye teba, misali cinya, naman wuya, damtsen hannu, tumbi da sauransu.

Da yake tsiro ne marar illa, bai cika girma ya yadu ba, domin zai iya kankancewa ya bace, shi ya sa wadansu likitocin sukan ce a bar shi a gani. Amma akan samu kashi daya cikin 100 na irin wannan tsiro ya zama daji ko da bai girma ba. Watakila wannan ne dalilin da ya sa likitocin tiyata sukan ba da shawara idan an gani a cire shi. Cire shin zai ba da dama a kai karin dakin gwaji a auna a gani a tabbatar shi ne ba wani tsiro ne mai illa ba.

 

Ni idan na kwanta barci sai in ji tafin kafafuwana sun dauki zafi kamar garwashin wuta. Ko matsala ce wannan?

Daga Alhaji G.B.S Kano

 

Amsa: Kwarai kuwa alamar wani ciwo ne wannan. Akwai cututtuka da sukan sa wannan wadanda yawancinsu sukan taba lafiyar lakar jiki ce. Wannan zogi daga lakar kafafuwanka ne. Don haka yana da kyau ka je a binciki mene ne.

 

Ni dalibi ne, to idan na dade ina karatu sai kaina ya rika ciwo. Ko me ke kawo haka?

Daga Aminu S. Kano

 

Amsa: Eh, akwai abubuwa kamar guda uku zuwa hudu da za su iya sa maka wannan. Na farko shi ne cewa watakila kwakwalwarka ba ta son abin da kake karantawa, na biyu shi ne watakila ba ka ci ka koshi ba a lokacin, na uku kuma shi ne cewa watakila a gajiye kake. Na karshe shi ne cewa watakila akwai matsala a idanunka, amma tunda ba ka ce suna ciwo ko ruwa ko kaikayi ko yin ja ba idan kana karatun, zai wuya a ce ido ne.

 

Ana ta ce mini na rame daga yin aurena. Sai na je asibiti aka yi mini aune-aune da gwaje-gwaje, suka fito na kai wa likita ya ce ba komai, amma sai ya ba ni wani magani in rika sha. Shi ne nake neman shawara ko gwajin suga za a yi mini?

Daga Shehu A. Katsina

 

Amsa: To yaya zai ce ba komai kuma ya ba ka magunguna? Da ka sani ka tambaya shin magungunan na mene ne aka ba ka, tunda gwaje-gwaje ba su nuna komai ba. Ka ga idan ka koma din ka samu ka sanar da shi sauran gwaje-gwajen da kake so a yi maka.

 

Ni kuma wasu jijiyoyi ne ke fito mini rada-rada tun daga wuya har ciki. Shi ne nake tambaya shin ko alamar wani ciwo ne wannan?

Daga Aminu L.

 

Amsa: Eh, kwarai za ta iya zama alamar wani ciwo, domin akwai cututtukan da kan sa jijiyoyin ciki da na wuya su yi rada-rada. Ka samu ka je likita ya gani ko za a gane na mene ne.

 

Idan na yi gudu ko tura mota nakan yi haki kamar raina zai fita. Na dai san ina cin goro. Ko yana iya sa haka?

Daga Abba FKD

 

Amsa: Eh, haki mai tsanani yayin gudu ko aikin karfi kamar tura mota alama ce ta wata matsala in ma dai a huhu ko a zuciya, ba cin goro ba ne. Da dai sigari ka ce. Idan ma zafin kirji ne ba haki ba, to wannan kai-tsaye a iya cewa matsalar zuciya ce ba huhu ba. Duk mai samun irin wannan sai ya je an binciki lafiyarsa an gano mene ne. Da ma akwai irin mutane masu cutukan huhu da zuciya da ba a so su rika yawan guje-guje ko aikin karfi da kan iya sa haki kamar rai zai fita.

 

Ni kuma da na yi aiki kadan sai zufa sosai.  Wadansu sai su ce wai lafiya ce. Ko haka ne?

Daga Umar Kano

 

Amsa: Eh, yawan zufa lokacin zafi ba wata matsala. In dai ba ka yi lokacin sanyi, lokacin da kowa ba ya zufa sosai a iya cewa lafiya ce.