Ni matar aure ce. Wadanne hanyoyi zan bi in magance matsalolin ciwon sanyi?
Daga B.S.
Amsa: Idan ke matar aure ce ya kamata ki san cewa maganin ciwon sanyi a mace mai aure shi ne cewa sai ke da mai gidanki kun sha magunguna gaba daya, domin idan mai gidanki ma na dauke da ciwon idan bai sha magani ya warke kamar yadda kika sha ba, to zai sake sa miki ne. Don haka zuwa asibiti ba ke kadai ba ne, tare za ku je a yi muku gwaji a ba ku magani. Idan matsalar ta tafi a duka ku biyun to fa shi ne za a ce an magance ta gaba daya
Ina da yaro dan wata 10 yana hakori yanzu, amma sai yawan zazzabi da ciwon ido da amai da zawo. Ina yawan kai shi asibiti, wani lokaci a dace wani lokaci ba a dacewa. To amma ina son shawara
Daga Maman Yara
Amsa: Tunda ana zuwa asibiti ana duba shi ana ba shi magunguna idan yana laulayin to ya yi kyau. Amma shawara ita ce ta hanyoyin kiyaye wa matsalolin tun da fari, wadanda muka sha fada a nan. Wadannan sun hada da allurar rigakafi, wato a tabbatar ya karbi dukan alluran da ya kamata, sai tsabtar gida, wato sharewa da gogewa tunda a wadannan watanni yaro yana rarrafe yana share gidan da hannayensa da gwiwoyinsa yana kai duk kazanta baki, amma idan gidan tas yake to, babu wannan hadari. Sai ba shi nau’o’in abinci masu gina jiki, domin su kara wa garkuwar jikinsa kwari, tunda a yanzu watanninsa sun kai ba bukatar mama kadai yake ba, har da abincin da cikinsa zai iya karba.
Mene ne sahihin bayani game da hutun haihuwa? Domin ni ina ganin mata na yi kuma ba a wanyewa lafiya. Misali makwabciyata da ta yi yau shekara 10 ke nan da tsayarwa amma ba labarin haihuwa kuma tana so ta haihu.
Daga Mai Damuwa
Amsa: Sahihancin bayanin shi ne cewa kowace mace da akwai tsarin da ya fi karbarta fiye da wani, tunda muna da tsari sun kai biyar ko shida na mata kawai, biyu kuma na maza. To macen da take wurin likitar mata aka yi mata tambayoyi a nan ne za a gano wane ne zai fi mata, ba wai ki ga wance an yi mata iri-kaza ba ki ce ke ma sai irinsa. Yawanci inda matsalar take ke nan, kawai wadansu matan da ka suke shiga abin ba tare da shawarar kwararriyar ungozoma ko likitar mata ba. Kuma ko da kwararrun ne ma suka bayar akan samu akasi bai yi ba, ko kuma ya kawo wata matsala, amma da an koma nan da nan za a canja zuwa wani. Mun sha fada cewa wannan tsari shi ne ainihin abin da ya cancanci a kira da cewa ‘sai an gwada akan san na kwarai,’ wato a mafi yawan lokuta sai an gwada iri biyu zuwa uku kafin a gano wanda ya fi karbar matar.