✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi

Wane tsari ne ake kira Inshorar Lafiya na Kasa (NHIS)? Ko yana da kyau mutumin da ya fito daga karkara ya shiga? Daga Basiru Danbazazzagi…

Wane tsari ne ake kira Inshorar Lafiya na Kasa (NHIS)? Ko yana da kyau mutumin da ya fito daga karkara ya shiga?

Daga Basiru Danbazazzagi

Amsa: Kwarai kuwa wannan tsari na kowa da kowa ne. Tsari ne da aka shirya domin ajiyar kudin bibiyar lafiyar mutum da iyalansa, kamar dai wani adashin gata. Ana shiga ne ta hanyar wasu kamfanoni da hukuma ta yarda da kafuwarsu wadanda ake kira Health Maintenance Organisation wato HMO. Kusan yanzu a kowane babban asibiti, wadannan kamfanoni (HMO) suna da ofishi domin biyan bukatun jama’a. Don haka idan akwai babban asibiti a kusa da kai, kuma kai mai zaman kanka ne, ba ka aiki a karkashin wani, ka je ka yi tambaya a nuna maka ofishin wadannan kamfanoni domin ka samu shiga wannan tsari. Idan kuma kana da wurin aiki, to wurin aikin naku za su iya sama maka irin wannan kamfani, sai a rika cire kudin da bai taka kara ya karya ba daga albashinka a duk wata.  Idan ka samu aka yi maka rajista, za a ba ka katin shaida wato ID Card, wanda za ka nuna duk lokacin da ka je asibiti. Idan ka yi rajista, to da kai da matarka daya da ’ya’ya hudu wannan rajista za ta yi wa amfani, wato mutum shida ke nan. Idan akwai wata matar da ’ya’ya kuma, su ma sai ka yi musu rajista tasu daban. Sai dai ba kowane asibiti ne za ka iya zuwa ba, sai wanda kamfanin da ka yi rajista yake da alakar yarjejeniya da su.

 

Idan na tashi daga barci a kullum sai na dauki wasu mintuna ba na ganin komai sai duhu kafin in fara gani. Shin wannan na nufin akwai matsala ce?

Daga Hadiza Machina

Amsa: Eh, kwarai kuwa matsala ce. Akwai abubuwa da dama da masana suka ce suna kawo irin wannan, yawancinsu a kwakwalwa, wasu kuma daga ido abin yake. Don haka sai kin je an binciki lafiyarki an tantance.

 

Me ke kawo ciwon makoshi, wani lokaci ma har a ji shi a kunne?

Daga A’isha Jibiya da Aliyu Nguru

Amsa: Kwayoyin cuta ne suka fi kawo irin wannan idan suka samu mafaka a makoshi, har su samu su shiga kunne ta wata kafa a nan cikin makoshi. Idan mutum yana samun irin wannan sai an duba an tabbatar kafin a ba shi magani

 

Me ya sa ba a mutunta masu kyamis? Na taba ganin an kama mai kyamis da magungunan zogi na paracetamol da diclof. Ko su ma suna da dokar sayarwa ne? A warware mini wannan lamari

Daga Hassan Ibrahim Warji

Amsa: Ai in dai ma’aikacin kyamis ba ya da lasisin sayar da magunguna dokar kasa ko ta jiha za ta iya aiki a kansa. Kawai dai ana samun sakaci ne a wasu lokuta ba a dabbaka dokar saboda wasu dalilai, har mutane suka dauka kowa zai iya shiga sana’ar da ka. Domin ko magungunan da aka yarda a sayar ba tare da sa hannun likita ba, mai sayar da su dole sai ya samu lasisi na sayar da magani. Irin wadannan masu sayar da magani a tsari kamata ya yi sai sun yi karatu na watanni ko shekaru sun samu satifiket sa’annan lasisi.

 

A da ina yawan ba da jini. To a yanzu na zo bayarwa sai aka gwada aka ce mini karfin jinin ya yi kasa. Ni na ga ban canja wani abincina ba amma dai a yanzu kullum sai na sha ruwan kwakwa. Shi ne nake tambaya ko akwai illa kan shan ruwan kwakwa?

Daga Musa GGC, Kano

Amsa: Eh duk da cewa ruwan kwakwa yana da sinadarin potassium, shan sa a kullum zai iya sa sinadarin ya yi yawa sosai a jini ya fara taba lafiyar zuciya. Wato ke nan ba kullum ake so a sha ba. Idan da kana yawan bin wannan shafi za ka san babu wata fa’ida a likitance mutum ya dauki wani abinci ko abin sha ya ce kullum sai ya sha ko ya ci. Ban da wannan kuma halin yau da kullum na rayuwa da shekaru da sauransu duk za su iya sa wa jini ya dan yi kasa ba tare da ka sani ba, amma bayan ’yan kwanaki sai ya iya dawowa daidai.

Ina jin wani abu na yawo a jikina kamar kiyashi wani lokaci kamar shocking, wani lokaci zafin jiki. Na je an yi mini gwajin ciwon sanyi da na hanta da na kanjamau da na fitsari ba a ga komai ba, shi ne nake tambayar ko akwai wani gwajin da ban yi ba.

Daga Yusuf Umar

 

Amsa: A’a ai ba kai ne za ka zayyana wa kanka irin gwaje-gwajen da za ka yi ba, zuwa za ka yi likita ya yi maka tambayoyi ya duba ka ya auna ka kafin ya rubuta wadanne gwaje-gwaje za ka yi. Wato watakila ka tsallake ganin likita wanda ya fi gwajin muhimmanci. Ga irin alamun da ka zayyana matsalar taka kamar ta shafi lakar jijiyoyin jiki ne. Ita kuma laka abubuwa da dama za su iya taba lafiyarta tun daga suga zuwa kiba zuwa kwayoyin cuta da sauransu.

 

Ban san abin da na yi ba likita ba ka amsa tambayata ba tsawon wata guda ke nan.

Daga Mustapha Habeeb

Amsa: Watakila tambayar ba za ta amsu ba ne a shafin jarida sai ka ga likita ido da ido ko ba a gane irin tambayar ba saboda rubutun ba ya karantuwa ko kuma an sha amsa irin tambayar a kwanakin nan.