Tsakanin allurar barci da ta kugu (ta ido biyu) wacce ce tafi ga mace da za a yi wa tiyatar haihuwa?
Daga A’isha Wada
Amsa: Ya danganta da abin da likitan da zai yi aikin ya fi so, sa’annan sai zabin wadda za a yi wa tiyatar. Wato zabin farko abin da aka fi so shi ne a yi shawara da likita a ji wanne ya fi, ko zabin da matar take so zai yiwu ko a’a, domin akwai lokutan da likita zai fi bukatar wata allurar a kan wata. Idan kuma ya ce duk daya ne a wurinsa, to sai matar ta zaba.
Ita allurar ido biyu fa’idarta ita ce mace ido biyu za ta kasance yayin tiyatar, tana ji kuma za ta iya ganin ma abin da ke faruwa idan tana so. Da an ciro jariri a take za a nuna mata. Sa’annan babu wata kwanciyar jinya idan aka gama, sai dai kawai a jira kafa ta dawo (tunda allurar tana kashe jin duk wani abu daga kugu abin da ya yi kasa), sa’annan ta fi araha. Sai dai kawai zafi a lokacin da ake yin ta da kuma ciwon kai da kan biyo bayanta.
Ita kuma allurar barci fa’idarta ita ce mace za ta yi barci, wato ta huta, ba ta ma san an yi ba, sai dai kawai ta farka ta ga jariri. Ita kawai matsalar ita ce sai an yi jinya mai dan tsayi kafin a farfado daga allurar ba kamar ta kugu ba. Kuma ta dan fi tsada kadan.
Nakan yawan samun matsalar rashin iya rike fitsari, wani lokaci har ya subuce ban sani ba idan ina aiki ko tari. Ko hakan matsala ce?
Daga Maman Khalil
Amsa: Eh, kwarai yawan sakin fitsari musamman lokacin tari ko wani aiki matsala ce musamman a mata wadanda suka dan manyanta ko wadanda suka haihu da dama. Amma ba daya take da matsalar yoyon fitsari ba, wadda kan faru a ’yan matan da suka samu matsala wajen haihuwa. Ita wannan matsala fitsarin ba zuba yake kai-tsaye ba, a’a sai an yi yunkuri kamar yadda kika ce, kamar yunkurin tari ko dariya, sabanin irin na ciwon yoyon fitsari wanda shi fitsarin yana zuba ne ba a iya rikeshi kwata-kwata.
Akwai hanyoyin da ake bi a taimaka wa mace mai irin wannan matsala, hanyoyin atisayen rike fitsari, akwai kuma tiyata idan hakan ta gagara. Yana da kyau mace mai samun irin wannan ta je likitar mata ta duba ta ta gani ko mene ne za a iya yi a maganc matsalar.