✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi

Na ga bayaninka a game da hanyoyin kariya daga cututtukan daji. Tambayata ita ce da gaske ne cututtukan daji wato kansa ba sa jin magani…

Na ga bayaninka a game da hanyoyin kariya daga cututtukan daji. Tambayata ita ce da gaske ne cututtukan daji wato kansa ba sa jin magani kuma ba sa son allura, wai za ta rika ta’azzara su?

Daga Bashir A. Kaduna

 

Amsa: A’a ba gaskiya ba ce. Akwai magungunan cututtukan daji na sha da na allurai kuma duk suna aiki sosai. Kai har ma tiyata ana iya yi a yi maganin daji ya tafi gaba daya, musamman idan a farkon tsirowar ciwon ne aka zo asibiti. Abin da watakila kake nufi shi ne ko ciwon daji na da magani idan ya bazu zuwa sauran sassan jiki. A nan ne ake da matsala a likitance, domin ana ganin ciwon dajin da ya bar wurinsa na ainihi inda ya fara tsirowa ya bazu a sassan jiki shi ne bai cika jin magani ba. Misali ciwon daji na huhu idan yana huhu za a iya masa tiyata a debe wurin, a kuma ba da allurai da magunguna ya tafi. Amma da zarar ya yadu ya bar huhu ya tafi kashin gadon baya misali, ko ya tafi hanta to ana ganin an makara.

Kwanakin baya ka yi magana a kan amfanin yawan shan ruwa. To ni kuma idan na sha ruwa a rana da safe sai na kai karfe hudu na yamma ban nemi wani na sha ba. Ko akwai wata shawara da za ta san a rika shan ruwa sosai?

Daga Abban Walid, Kabo

 

Amsa: Eh, kwarai kuwa yawan shan ruwa yana da amfani ga lafiyar jiki sosai, musamman ma a lokutan zafi, inda aka kiyasta ana so mutum ya sha ruwa a kalla lita biyu a rana, ba dole sai a lokaci guda ba, wato idan aka hada duka ruwan da mutum ya sha a rana ana so ya kai lita biyu. Sai dai saukin a nan shi ne ba wai dole sai ruwa kadai ba, a’a za ka iya shan wasu abubuwa masu ruwa kamar shayi ko lemo marasa sukari sosai. Idan mutum yana shaye-shayen abubuwa masu ruwa a rana ba lallai ba ne ya ji kishirwa sosai ba. Akwai mutane irinka da kusan sau daya suke shan ruwa mai sunan ruwa, amma suna yawan shan abubuwa masu ruwa-ruwa. To kai ma idan kana yawan shan irin wadannan abubuwa masu ruwa-ruwa sosai to babu matsala.

Na taba karyewa a kafa amma na warke. To idan na dauki kaya masu nauyi sai in ji wurin yana yi min ciwo kadan shi ne nake neman shawara.

Daga Khalifa Boy

 

Amsa: Abin da aka fi so shi ne duk wanda aka ce an yi wa aikin tiyata babba kamar na karayar kafa, kafin a sallame shi ya kamata ya tambayi likitocin da suka yi tiyatar ko shin zai iya komawa bakin aikinsa da harkokinsa da ayyuka da daukar nauyi da sauransu ko kuwa? Don haka likitanka ne ya kamata ya ba ka gamsasshiyar shawara, tunda shi ya ga irin karayar ya ga kuma irin warakar da ka yi.

Duk da haka dai masana lafiyar kashi sun yi amanna cewa duk lokacin da aka yi wa mutum tiyatar kashin kafa ba zai koma aiki ko fara daga kayan nauyin da ya saba dagawa kafin karayar kai-tsaye ba, sai ya dauki lokaci da kuma a bangare daga nauyi sai ya yi atisaye. Atisayen kuwa shi ne idan aikinsa ya danganci daga kayan nauyi, dole sai ya fara daga abubuwa marasa nauyi idan ya warke, sa’annan sannu-sannu ya rika karawa bayan wasu lokuta. Misali idan mutum yana iya daukar abubuwa masu nauyi kamar buhun siminti mai nauyin kilo 50 kafin ya karye a kafa, idan ya warke idan ya ga buhun siminti ya guje shi, sai dai ya daga abubuwa wadanda ba su kai shi ba, kamar abubuwa masu nauyin kilo 10. Sai bayan watanni wurin ya yi kwari ya kara ya iya daga masu kilo 20 kuma misali, a haka duk bayan watanni sai ya kara wata gomar har zuwa nauyin da idan ya kara ba zai ji zafi a wurin ba, saboda a bai wa kashin lokaci ya saba da daukar nauyi. Ba kwatsam kawai lokaci daya da an sallami mutum ya ce zai iya harkokin da yake yi a da ba.

Haka ma dokar take a sauran mutane na wasu bangarorin rayuwa bayan an yi musu mutum tiyata. Misali manomin da aka yi wa aikin tiyatar kaba, ba a cika so ya koma gona ba, sai dai idan noman zamani zai yi wanda ba ya bukatar karfi, kamar da tarakta. A wasu wuraren ma akan rage wa mutum yawan aikinsa ne idan aka yi masa tiyatar. Misali, idan za ka iya tunawa bayan an yi wa tsohon dan wasan kwallon kafar Najeriya Kanu Nwankwo tiyata a zuciyarsa ai ya koma buga kwallo, sai dai idan ka lura ba a sa shi ya buga cikakken wasa. Haka da direban mota mai nisan zango aka yi wa irin wannan tiyata za a ce ya bar tukin nisan zango, ya dawo na cikin gari. Sa’annan ko a masu aikin da ya jibanci aikin zama kawai kamar na ofis, idan aka samu wanda aka yi masa tiyata a kashin kugu ko na gwiwa, yawanci akan ce musu kada su sake harde kafa idan za su zauna, wato ba su ba dora kafa daya a kan daya don kada aikin ya sake gocewa. Haka nan akwai wasu tiyata na kashi da za su sa dole ma mutum ya canja aikinsa gaba daya ko kuma ya yi ritaya, tunda a tsari idan kwararren dan kwallo ya karye a kwauri, ai ka ga kafin a yarda ya buga manyan wasanni ko da ya warke sarai, sai an dade.

Ni mace ce mai aure da ’ya’ya har uku, amma ba ni da jiki sosai. Ina so in dan yi jiki shi ne nake so a rubuta mini maganin da zai sa in yi jiki ko kuma a ba ni shawara.

Daga Maman Sadik

Amsa: Shawara ita ce ki je asibiti likita ya auna nauyinki da tsayinki a gani koda gaske ne nauyinki bai kai yadda ake so ba, sa’annan watakila a ba ki magungunan da za su kara miki cin abinci (ba maganin kara kiba ake bayarwa ba). Idan aka auna aka ga nauyinki daidai yake da wuya a ba ki wasu magunguna, domin ba ki da bukatarsu.