Gobe Asabar wato 17 ga Nuwamba ita ce ranar tunawa da bakwaini a duniya. A 17 ga Nuwamba ta kowace shekara hukumomin lafiya a duniya suke tunawa da lafiyar jarirai bakwaini. A irin wannan rana akan fadakar da iyaye mata su san irin matsalolin da yaran da ba su gama girma a ciki ba kan fuskanta idan sun zo duniya ba shiri, don a san matsalolin a kuma kiyaye su ko magance su. Ban da cututtukan da kan kama yara a yarinta, kasancewa bakwaini kadai na saka yara cikin hadarin saurin mutuwa.
Babbar matsala ta hadari ta farko da bakwaini kan fuskanta ita ce matsalar numfashi. Wannan ta samo asali ne tun daga halittar huhu inda shi huhun jarirai yake bukatar cika akalla watanni takwas zuwa tara kafin ya rika.
To da zarar an haifi jariri a watanni bakwai za a fara lura da numfashinsa kamar ba daidai da na rikakkun jarirai ba, don haka ne akan ga numfashinsu da sauri-sauri kuma yana fita da kyar. To wannan ita ce babbar abin damuwa. Ko a gida ke nan aka haifi bakwaini idan aka ga irin wannan matsalar numfashi dole a kai jariri asibiti. Wasu kuma za a iya yin sa’a a ga numfashinsu kamar daidai (a wadanda aka yi wa iyayensu allurar rikar huhu kenan ta dedamethsone).
Matsala ta biyu da ya kamata a sani ita ce ta rashin tsotso. Ba kowane bakwaini ba ne zai iya tsotso kamar sauran rikakkun jarirai, don haka za a iya ganin bakwaini ya kama tsotso amma yana saurin saki saboda gajiya, wato abin na ba su wahala. Za a ga ba su kara nauyi a kullum. Wannan alama ce ta cewa ba ya samun ruwan nono sosai, sai dole an fara matsawa a kofi ana ba shi da sirinji. A asibiti za a iya taimaka wa uwa da irin wannan.
Sai matsalar jin sanyi wato rashin dimin jiki. Kowane jariri yana da saurin jin sanyi amma bakwaini sun fi sauran jarirai yawan jin sanyi saboda fatarsu ba ta rika ba. Don haka sai an ribanya kayan jin dimi a bakwaini. Wannan ce ma ta sa a asibiti akan ga ana sa su a wata ’yar kwalba ta jin dimi na wasu ’yan satuttuka, kamar dai suna cikin uwa.
Wata matsalar ita ce ta saurin kamuwa da cututtuka fiye da sauran jarirai rikakku. Don haka ne ma ba mu cika son damuke-damuken bakwaini ba (irin na ’yan barka) har sai sun cika watanni biyu ko ma fiye da haihuwa, don kada a yada musu cututtuka.