Idan mace ta samu ciwon daji wato kansa, sai aka samu wata a cikin ’ya’yanta ma ta samu irin ciwon, shin hakan yana nufin sauran ’ya’ya matan na dauke da kwayoyin halitta na cutar?
Daga Ibrahim S, Kaduna
Amsa: A’a ba dole ba ne a ce sauran ’ya’ya matan na dauke da kwayoyin halitta na gadon kansa idan mahaifiyarsu da yayarsu suka samu matsalar ba. Domin ita harkar gadon kwayoyin halitta tana da sarkakiya, wato ana iya tsallake daya ko biyu daga cikin sauran ’ya’yan ko ya zamo a samu duka suna da birbishin ciwon, ko ma a samu cewa dukansu babu ko da birbishin ciwon dajin.
A irin wannan yanayi shawarar da ake ba wa irin wadannan mata wadanda iyayensu mata da yayyensu suka samu matsalar ciwon daji ita ce, sai dukansu su samu kwararren asibitin mata su je a auna kananan halittunsu na DNA a gani ko suna dauke da wadannan kwayoyi na gado ko a’a. Misali, idan ciwon daji na mama ne akwai gwaji na BRCA Gene Test, idan na bakin mahaifa ne ana yi musu wani gwaji na Pap Smear duk bayan shekaru uku misali. Idan aka ga birbishin ciwon ana tarar matsalar ta hanyar cire abin da ake ganin ba makawa zai samu ciwon daji. Sanannen misali irin wannan shi ne na sananniyar jarumar fina-finan Amurka da mahaifiyarta ta samu kansa, aka je aka yi mata gwaji aka ga tana da birbishin kwayoyin gado na ciwon ita ma. Aka ba ta shawarar cire mahaifarta da mamarta kuma ta cire. Ga shi nan tana zaune lafiya.
Amsar Sadeek A. Sakkwato: Idan muna tare ita ce cewa ba matsala ba ce abin da kake tambaya a kai.
Wai da gaske ana son barcin maza ya fi na mata yawa kamar awa 7-8 a maza, mata awa 5-6?
Daga Maman Ummi, Kaduna
Amsa: A’a akasin abin aka fada miki. Wato mata ne suka fi maza bukatar hutu da bukatar samun barci mai tsayi saboda yawan sarkakiyar da ke tattare da kwakwalwarsu.
Wai me ya kamata in bai wa jaririna domin ya yi kiba? Domin na kai shi asibiti an ce kalau yake, amma ina so in ga ya ciko.
Daga Maman Baby
Amsa: A’a, haba Maman Baby ai yanzu ke ya kamata a tambaya shin a ganinki me za ki ba shi ya cicciko, domin iyayenmu sun ma fi wadansu likitocin masaniya a kan cimakar jarirai, kuma ganin cewa mun sha kokartawa muna jero abubuwan da za ki iya ba jaririnki a wannan shafi, ina ga idan na sa ki wani dan aikin lissafo mana ire-iren abincin da za ki ba shi ki aiko ta tes ba za ki gaza ba. Kin ga idan aka wallafa a nan sai wadansu ma su karu.