✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amaryar Soja ta fara bore!

Ni kaina na san ba ajima ba ce amma na dage da neman aurenta.

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa.

Ga ci gaban labaran auratayya da muka samu daga masu karatu idan aka yi tambayar yaya za a shawo kan amaryar da fara bore?

Anty Nabila ki sama mani mafita, ga labarin aurena kamar haka:

Ni matashin sojan Najeriya ne, ina matukar son aikina, ba na jin zan iya wani aiki a duniyar nan in ba aikin soja ba, domin sau biyar ina kokarin neman shiga aikin amma ban samu ba sai karo na shida, kuma da a ce ban samu ba zan ci gaba da nacin kara nema har sai na samu.

Kamar yadda na nace wajen neman aikin soja, to, haka kuma na nace wajen neman auren matar da muke tare a yanzu.

Ta kasance daga babban gida domin mahaifinta babban ma’aikacin Gwamnatin Tarayya ne, yayin da ni kuma mahaifina karamin manomi ne.

Amma dai iyayenmu mata sun kasance ’yan uwan juna, a dalilin zumuncin da ke tsakaninmu ne muka san juna har muka fara soyayya.

Ni kaina na san ba ajima ba ce amma na dage da neman aurenta.

Da farko iyayenta sun goya min baya, amma ganin masu kudi da masu fada-a-ji sun fito neman ta sai ya sa ’yan uwanta, har da mahaifiyarta wacce tana matsayin umma a gare ni suka juya min baya.

Suka nuna sai dai ta zabi daya daga cikin masu kudin nan da suka fito nemanta, suka rika ce mata, me za ta yi da ni kurtun soja, albashina bai isa ta balle har in yi mata wani abu?

Suka dinga zuga ta cewa wai duk soja dan giya ne, kuma bugun mata na ga soja. Amma duk ta ki biye masu ta ce ita dole sai ni za ta aura.

Wasu daga cikin ’yan uwanta suka ce duk inda suka gan ni sai su halaka ni saboda na hure mata kunne na ki barinta ta yi aure na ji da fada.

Ni kuma da na ji haka na yi takakkiya na je garin nasu daga garin da nake aiki don in ga mai iya halaka ni daga cikinsu, don ni ba ni jin tsoron kowa sai Ubangijin da Ya halicce ni.

Na yi mako daya a garin kuma a gidansu aka yi min masauki, kullum muna tare barci kadai ke raba mu. Kuma duk masu cika bakin za su halaka ni ko kallon banza ba su iya yi mani ba.

Daga nan dai tafiya ta mika, aka nemi in turo magabatana, cikin wata uku aka yi komai aka gama muka zamo ma’auran juna ni da ita.

Na kama mata gida a garin da iyayenta suke. Yanzu haka danmu watansa shida, kuma kullum ina jin karin soyayyarta a cikin zuciyata ita ma kuma haka.

Tunda muka yi auren aka tura ni cikin daji wajen yaki da ’yan ta’adda, don haka ba mu taba zama na dogon lokaci tare ba. Sai dai in na samu lokaci in kai mata ziyara in koma, don haka kullum cikin kewar juna muke.

Yanzu haka dai na kawo mata ziyara, amma kwatakwata ba zaman lafiya a tsakaninmu, magana daya biyu sai ta ce min ita ta gaji, ita ga ta da aure amma ba ta da miji.

Ita sai dai in baro cikin daji in dawo bariki, ita ba ta son aikin soja, ita yaronmu zai tashi bai san wane ne Babansa ba, ita yanzu in aka harbe ni haka nake son ta rayu ita daya?

Haka take ta yi min mita, kuma kowane da kuka take rufewa, wanda hakan sai ya karya min zuciya, ni ma in ji ina kwalla saboda tsananin son da nake mata.

Yanzu gobe zan koma cikin daji, amma hankalina a tashe saboda ba na son mu yi rabuwar baran-baran da ita.

Ni dai ba na jin zan iya wani aiki a duniya in ba aikin soja ba, ita kuma ko saboda yarinta ne ta kasa fahimtar cewa aikina wani muhimmin bangare ne a rayuwata, tana son in sadaukar da aikina saboda farin cikinta.

Shin bai kamata ita ma ta sadaukar da son ranta saboda samar mani natsuwa ba? Ashe dama haka soyayya take?

Ina neman shawararki Anty Nabilah, don Allah ki sama mani mafita daga wannan rikitaccen al’amari.

Kuma ina son ki mika sakona ga Baba Buhari da sauran mahukuntan Najeriya da su rika la’akari da mu sojojin da ke cikin daji, a rika ba mu dama muna sauke nauyin iyalanmu.

Yanzu ni shekarata uku a cikin daji sai dai a ba ni ’yan kwanaki kalilan in zo in ziyarci iyalina, ko da minti daya na gota kwanakin da aka diba min ban koma cikin daji ba hakan na iya zame mani matsala.

Muna cikin dajin nan sai mu yi kwanaki ba abinci ba ruwan sha, ledar ruwa guda ga kowane soja uku, amma sai mu ga jirgi ya wuce mu ya sauke kayan abinci ga ’yan ta’adda.

Ina son aikina amma ina jin kamar aikin banza nake yi saboda wadanda suka tura mu yakar ’yan ta’adda sun kasance su ne iyayen gijin ’yan ta’addar.

Amsa: shawarata gare ka ita ce ka ci gaba da hakuri, ka kuma rika lallaba ta da lallashinta, watakila dawainiyar haihuwar fari ya dan dagula mata tunani, ga kuma yarinta kamar yadda ka fada.

Don haka karin hakuri da kai zuciya nesa da dagewa da addu’a su ne mafita, a hankali wata ran za ka ga abin ya wuce insha Allah!