✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Almajiri ya rasu bayan fadawa a kududdufi a Kano

Wani almajiri mai shekara 13 ya rasu bayan da ya nitse a cikin kogi a kauyen Makugara da ke Karamar Hukumar Karaye a Jihar Kano.

Wani almajiri mai shekara 13 ya rasu bayan da ya fada a cikin kogi a kauyen Makugara da ke Karamar Hukumar Karaye a Jihar Kano.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce almajirin mai suna Yusuf Magaji ya gamu da karar kwana ne a lokacin da shi da sauran abokansa alamjirai suke wanka a bakin rafin.

Kakakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya bayyana cewa almajirin da sauran abokansa daga tsangayar Malam Nafiu Na Adama suna tsaka da wanka a gefen rafin ne santsi ya kwashe shi ya fada a ciki.

Ya bayyana cewa malamin tsangayar ne ya yi wa hukumar kiran gaggawa ya sanar da ita cewa almajirinsa ya fada a cikin rafi.

A cewarsa, almajiran suna hanyarsu ta komawa kauyen ne suka tsaya domin su yi wanka a gefen rafi, amma aka yi rashin sa’a mutum daya daga cikinsu ya fada a ciki.

Kakakin hukumar ya ce jama’a sun yi nasarar ceto almajirin a galabaice, suka garzaya da shi Asibitin Kwararru na Karaye. Daga bisani likitoci suka sanar cewa rai ya yi halinsa.

Abdullahi ya ce a mika gawar mamacin ga Malam Nafi’u Na Adama, domin gudanar da jana’izar almajirin nasa.