✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yiwuwar dan Gaddafi ya tsaya takarar shugaban kasa a Libya

“Saiful-Islam dai bai sanar da cewa zai yi takarar ba a hukumance, amma ’yan Libya da dama za su bukaci ya tsaya takarar.”

Akwai yuwuwar dan tsohon Shugaban Libya, marigayi Muammar Gaddafi, Saiful-Islam ya tsaya takarar Shugaban Kasar a zaben dake tafe a kasar, kamar yadda tsohon kakakin tsohon shugaban ya sanar.

A ranar 15 ga watan Fabrairu ne dai kasar Libya ke cika shekaru 10 tun bayan zanga-zangar da ta kai ga kifar da gwamnatin tsohon shugaban a 2011.

Bayan kifar da gwamnatin ne dai ’yan tawaye suka shiga farautar marigayi Gaddafi da iyalansa, lamarin da ya kai ga hallaka shi da dansa, Mutassim.

Kazalika, an hallaka wani dan nasa, Khamis a wani harin bam a birnin Tripoli, yayin da shi kuma Saiful-Islam ya kasance a tsare a gidan yarin kasar har zuwa watan Yulin 2017.

Kakakin tsohon Shugaban Kasar, Moussa Ibrahim ya ce an haramtawa magoya bayan Gaddafi shiga siyasa a kasar, duk da cewa sune mafiya rinjaye a kasar.

Ya ce, “Yana neman takarar ne saboda ya zama alamar hadin kan kabilun Libya da kungiyoyin siyasar kasar.

“Saiful-Islam dai bai sanar da cewa zai yi takarar ba a hukumance, amma ’yan Libya da dama za su bukaci ya tsaya takarar,” inji Ibrahim Moussa.

Ana sa ran dai cewa za a yi zabe a kasar ranar 25 ga watan Disamba, yayin da gwamnatin rikon kwarya za ta ci gaba da tafiyar da al’amura a kasar har zuwa lokacin.