✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai gawarwaki 102 da ba a san danginsu ba a asibitin Abuja

Asibitin ya ce in 'yan uwansu ba su zo ba, za su binne su

Akalla gawarwaki 102 ne da ba a san danginsu su ba yanzu haka ke ajiye a sashen adana gawarwaki na babban Asibitin Kubwa a Babban Birnin Tarayya Abuja. 

A wata sanarwa da hukumar gudanarwar asibitrin ta fitar ranar Litinin, ta ce ‘yan sandan ne suka kawo gawarwakin daga sassan Abujan daban-daban daga tsakanin shekarar 2019 zuwa 2022. 

Kazalika sanarwar na nuna a shekarar 2019, an kawo gawarwaki 19 asibitin, sai a 2020 guda 10, sai kuma 2021 da aka samu mafi yawa wato 59, yayin da a shekarar 2022 aka samu guda 14. 

 Sanarawar ta ce, “Muna sanar da mutane cewa duk wanda ya san yana da alaka ko ya san wadannan gawarwaki da ya garzayo Asibitin Kubwa sati uku bayan wallafa wannan sanarwar domin karbar gawar.”

Hukumar gudanarwar dai ta ce da zarar wa’adin da ta bayar ya cika kuma ba a samu wadanda suka zo suka karbi gawarwakin ba, to sai dai su mika su ga hukumar da ta dace domin binne su. 

Aminiya dai ta gano a kunshin sanarwar da hukumar gudanarwar asibitin ta wallafa babu sunayen gawarwakin da ta ce masu alaka da su din su zo su karba don binnewar.