✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai ayyukan rashawa 7,340 da muke bincike a kai – EFCC

(EFCC) ta ce har yanzu akwai ayyukan rashawa sama da 7,340 da har yanzu take bincike a kan su

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ce har yanzu akwai ayyukan rashawa sama da 7,340 da har yanzu take bincike a kan su daga cikin korafe-korafe 10,152 da ta karba ya zuwa watan Disamban 2020.

Mai rikon mukamin shugaban hukumar, Mohammed Umar Abba ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba cikin sakonsa na karshen shekara.

Shugaban ya ce hukumar ta sami nasarar gurfanarwa da kuma samun yanke hukunci a kan kararraki 865 daga cikin 1,305 da ta shigar a kotuna daban-daban cikin shekarar 2020.

Mohammed ya kara da cewa hukumar ta kuma kwato makuden kudade da kadarori daga mutanen da aka yanke wa hukunci kan laifukan rashawa.

Shugaban ya kuma bayyana shekarar 2020 a matsayin wata zakarar gwajin dafi, duk da cewa annobar COVID-19 ta kawo musu tsaiko kan abubuwan da hukumar ta yi harsashen aiwatarwa.

Ya ce, “Kullen Korona ya jawo koma-baya a ayyukan mu matuka. A cikin sama da shekaru 17 da kafa mu, ba mu taba fuskantar kalubalen aiki irin na bana ba,” inji shi.

Daga nan sai kuma ya yi kira ga ma’aikatan hukumar kan su kara jajircewa wajen yaki da rashawa, yana mai cewa idan EFCC ta gaza, yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ya ruguje.