✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Akwai alheri a sana’ar saka tufafi ta gargajiya – Usman Adamu Dongs

Usman Adamu Dongs matashi ne da ke sana’ar saka, wadda ya ce ya gaje ta ce daga wajen mahaifiyarsa sama da shekara 20 da suka…

Usman Adamu Dongs matashi ne da ke sana’ar saka, wadda ya ce ya gaje ta ce daga wajen mahaifiyarsa sama da shekara 20 da suka gabata. A zantawarsa da Aminiya ya bayyana yadda suke saka tufa daga audugar da suke kadawa su saka ta zama yadi a dinka riga da wando da hula sa sayar daon sanyawa a lokutan taron gargajiya:

Yaushe ka fara sana’ar saka?

Yanzu da fara sakar da nake yi na kai shekara 20; kuma mahaifiyata ce ta koya mini tun ina karami.

Sakar kawai kake yi ko duk da dinki?

Ba wanda ba na yi. Ina sakawa kuma ina dinkawa a biya ni domin wannan sana’a ita ce hanyar cin abincina.

Idan ka saka kana sayarwa ne ko kawai sai in an sa ka sakar?

Idan na saka ina dinkawa ina kuma sayarwa ina kuma sakawa in ajiye domin wani lokacin akan zo neman fallen cikin gaggawa za a dinka ba a samu; amma idan aka samu fallen sai a biya ni in dinka.

Wane rufin asiri ka samu a sakar?

Gaskiya akwai domin ana samun yadda za a tallafi rayuwa a wannan lokaci sai dai da yake a gargajiyance muke yi ba kullum muke samun yadda za a yi din ba sai dai godiyar Allah. Amma muna kira ga gwamnati ta tallafa mana domin kayan su rika fita kasashen waje don ganin an daukaka al’ada; wanda yin hakan zai kara taimaka mana sosai asirinmu zai kara rufuwa.

Kamar audugar nawa kake iya saka fallen da zai yi riga da wando da hula?

Tana kaiwa audugar Naira dubu biyu. Idan na hada kuma ina sayarwa Naira dubu 16, idan na dinka har da gare. Kuma ina sayarwa dubu 50 zuwa dubu 60 akalla.

A kwana nawa kake iya gama sakar kafin ka dinka?

Ba ya wuce kwana uku na gama saka, sai in hada kuma har in gama ba na sa kayan Bature wato allura da zare. Allurar da muke aiki da ita ita ce aka huda.

Kai kake kada audugar ka saka da kanka ko yi maka ake yi?

Mahaifiyata take kada min audugar, ni kuma in saka in hada.

A karshe me za ka ce ga wadanda suka yi watsi da sana’o’in gargajiya?

Ina kira kan su dawo su rungumi sana’o’in gargajiya, mu kuma muna rokon gwamnati ta kawo mana dauki. Domin sana’armu ta gado ta inganta mu ci gaba da bunkasa sana’o’in gargajiyarmu.

%d bloggers like this: