✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aisha Binani ta suya sheƙa daga APC zuwa ADC

Binani ta yi wa sabuwar jam'iyyar tasu ta haɗaka fatan samun nasara.

Tsohuwar Sanata kuma ’yar takarar gwamna a Jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu Dahiru Binani, ta sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta ADC.

A cikin wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, an ga Binani tana yi wa wasu matasa jawabi, inda ta bayyana goyon bayanta ga sabuwar jam’iyyar.

“Mun zaɓi jam’iyyar ADC kuma za mu ci gaba da tafiya a cikinta,” in ji Binani.

“Muna roƙon Allah Ya raba mu da waɗanda suke cikinmu amma suna ɓata jam’iyya.”

Bayan ta gama jawabin nata, an ga hotunan ta tana riƙe da katin zama mamba na jam’iyyar ADC.

Binani ta tsaya takarar gwamnan Jihar Adamawa a 2023 ƙarƙashin jam’iyyar APC, inda ta fafata da Gwamna Ahmadu Fintiri na PDP, amma ba ta samu nasara ba.

Zaɓen na 2023 ya bar baya da ƙura, idan babban jami’in INEC ya ayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaɓen tun kafin kammala tattara sakamakon zaɓen jihar.

Daga baya INEC ta dakatar da shi tare da ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba.

Bayan sake zaɓe a wasu yankuna na jihar Fintiri ya samu nasara tare da kayar da Binani.