✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ainihin abin da ya faru bayan ’yan bindiga sun tare mu —Sheikh Guruntum

Sheikh Tijjani Guruntum ya bayyana abin da ya faru a lokacin da ’yan bindiga suka tare su

Fitaccen malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum, ya bayyana yadda ayarin motocinsa suka fada a tarkon ’yan bindiga da kuma abin da ya faru tsakaninsu.

Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum ya bayyana hakikanin abin da ya faru a harin da bata-tarin suka kai musu a Jamhuriyar Nijar ne bayan an yi ta yada-karairayi game da lamarin a kafofin sada zumunta.

Ya bayyana cewa ayarin motocinsu da suka je suka gabatar da darusssa a Jamhiryar Nijar sun fada a tarkon ’yan bindiga ne a hanyarsu ta dawowa Najeriya, amma dukkansu Allah Ya kubutar, babu ko kwarzane.

“Dukkanmu mun dawo gida lafiya, da ni da Dokta Mansur Isah Yelwa da Malam Sagir da Malam Amir da Alaramma Abdulrahim Mansur Isah Yelwa, duka mun dawo gida lafiya kalau babu wani abu.

“Su ma ’yan uwa malamnmu na can Nijar wadanda muka taho da su, suka yi mana rakiya, muka yi (darussan tare) da su, babu abin da ya sami wani daga cikinsu. Alhamdulillah, in ji Sheikh Guruntum.

Malamin ya yi bayanin abin da ya faru dalla-dalla a majalisinsa da ke Bauchi, bayan dawowarsu Najeriya, domin karyata jita-jitar da aka yada game da abin da ya faru.

Ya ce ya yi bayanin ne ganin yadda, “Wadansu suke yada abubuwa masu tashin hankali, muka ga ya zama dole a kanmu mu yi kokari mu yi bayani a takaice, abin a yake shi ne gaskiyar magana.”

Yadda muka yi arba da ’yan bindiga

Ya ce lamarin ya faru ne bayan sun kammala gabatar da darussan kwana uku a Nijar, ranar Talata, washegari Laraba da safe suka kamo hanyar dawowa gida.

Sheikh Guruntum ya ce, “Gaskiya ne ’yan bindiga sun tsare mu a safiyar yau (Laraba), bayan fitowarmu muna kan hanya tare da sauran malamai da ’yan uwa da muka tafi gaba daya, [’yan bindiga] suka zo suka kewaye mu a kan hanya, da bindigoginsu suka tsare mu.

“Lokacin da suka tsare mu, abin da suka fara yi, na farko shi ne kokarin bude motar, amma da yake ‘central lock’ ne ba zai budu ba sai dole ta ciki.

“Da suka ji ba za ta budu ba, sai suka ce mu bude motar ko su bude mata wuta. Amma ba mu bude mota ba, duka [mu da ke ciki] mun daidaita [a kan cewa] ba za mu bude mota ba.

“Muna cikin wannan ce-ce-ku-ce, [sai] daya daga cikin motocin da ke cikin tawagarmu ta baya — wanda Malam Sagir yana cikin motar, motar Alhaji Jibril — sai suka juya.

“To dama kofar ragon ne [’yan bindigar suka yi], sun so duka motocin su shigo ne; Ganin waccan motar tana kokarin ta juya, sai suka yi kanta da harbi.

“To cikin taimakon Allah, waccan motar, juyawarta, direbanmu da ya ga hankalinsu ya koma can, sai ya zaburi motarmu.

“Cikin taimakon Allah, duka Allah Ya kubutar da mu, babu wanda aka yi wa rauni, babu wanda aka yi wa kwarzane, babu wanda wani abu ya same shi,” in ji Sheikh Guruntum.

Sai dai ya bayyana cewa wutar da ’yan bindigar suka bude ta sami wasu mutum biyu da ke cikin wasu motoci da ke bayan ayarin motocinsu, amma ba tafiyarsu daya ba.

Ya kara da cewa, “Akwai wadansu bayin Allah da su ba a cikin tawagarmu suke ba, sun shigo cikin (harin), harbin ya shafe su bayanmu, wanda mun samu labarin an sami mutum biyu daga cikinsu, amma mun samu labarin [cewa] ba rauni ne mai tsanani su ma suka yi ba.”

Jami’an tsaro sun kawo dauki

Sheikh Guruntum ya kuma bayyana cewa, jami’an tsaro na Jamhuriyar Nijar sun kawo dauki a kan kari, bayan harin.

Ya ci gaba da cewa, jami’an tsaron, “Sun ba da gudunmawa matuka, Allah Ya saka musu da alheri.”

“Su ma malamanmu na kasar Nijar da suka rako mu, muka gabatar da (darussan) tare babu abin da ya same su.