✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

AFCON 2021: Burkina Faso ta tsallaka mataki na gaba

An dai tashi wasan ne 1-1.

Burkina Faso ta samu nasarar tsallakawa mataki na gaba a gasar cin kofin Afirka da ke gudana a kasar Kamaru bayan ta doke tawagar kwallon kafar Gabon.

An dai tashin wasan ne da ci 1-1 wanda hakan ta kai ga bugun fenareti bayan an yi gumurzu na tsawon minti 120.

Ismahila Ouedraogo ne ya jefa wa Burkina Faso a bugun fenaretin da sakamakon ya kai an karkare shi  7-6.

Kyaftin din Burkina Faso, Bertrand Traore ne ya jefa mata kwallon farko a minti na 28 bayan ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaron raga da tawagar ta samu a minti na 18 da soma wasan.

Ita kuwa tawagar Gabon wadda ta ga samu ta ga rashi, ta koma buga wasan da ’yan wasa 10 bayan an daga wa Sidney Obissa katin sallama a minti na 67 saboda keta da ya yi.

Sai dai hakan bai sa ta yi kasa a gwiwa ba inda dan wasanta, Ecuele Manga ya farke kwallon da Burkina Faso ta jefa mata wacce alkalin wasa ya bayar da hukuncin cewa Adama Guira ne ya ci gida.

A ranar Asabar, 29 ga watan Janairu ne dai tawagar ta Burkina Fasa da ake yi wa lakabi da The Stallions, za ta hadu da daya daga cikin tawagar da ta yi nasara tsakanin Najeriya da Tunisia wadanda su ma suna can suna barje gumi a wasan matakin yan shida wanda shi ma siri daya kwale ne.