✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Addu’o’i ne za su kawo karshen ta’addanci a Arewa’

An yi kira ga al’umma kasar nan musamman a yankin Arewa da ayyukan ta’addanci suka yi wa katutu da su tashi domin yin addu’o’in neman…

An yi kira ga al’umma kasar nan musamman a yankin Arewa da ayyukan ta’addanci suka yi wa katutu da su tashi domin yin addu’o’in neman kawo karshen wannan bala’i.

A wajen hudubar sa ta sallar juma’a a yau a masallacin Juma’a na Kofar Guga da ke cikin garin Katsina, limamin masallacin Malam Badamasi Abbas ya ce, addu’o’in cikin dare a yanzu ya kamata al’ummar musulmi za su ci gaba da yi domin rokon Allah ya yaye mana wannan iftila’i.

“Zargi ko aza wa wani mutum ko mutane ko wani sashe laifin halin da muke ciki na rashin tsaro a arewa ba shi ne mafita ba.

“Mu koma ga Allah tare da rokonsa musammam wajen yin addu’o’in cikin dare ko ya jikanmu ya dauke mana wannan matsala da kullum take cikin rayuwarmu.”

Malamin ya ce, neman gafarar Allah ita ce kan gaba a yanzu domin abin ya wuce tunani ko hankalin duk wani mai hankali.

Saboda haka malamin ya yi wannan kira hatta ga wadanda ba musulmi ba domin in masifa ta shigo babu ruwan ta da addini ko wani abin da mutun yake tunani akan shi domin tana shafar har wanda bai san da ita ba.

“Yin shiru mu ce za’a kawo karshen wannan bala’in daga kowane sashe ba shi ne mafita ba, amma mu koma ga mai ikon komi domin ya dauke mana wannan masifa”, inji Malam Badamasi Abbas.