Gwamnatin Jihar Adamawa ta biya Naira miliyan 20 a matsayin kasonta na aiwatar da shirin noman Fadama Kashi na 3 Zubi na Biyu na karin Kudin Shirin (AFII) don hanzarta karfafa yunkurin dawo da hanyoyin rayuwa ga jama’ar jihar.
Shugaban shirin na jihar, Malam Mohammed Bello ne ya sanar da haka a ranar 17 ga Nuwamba a Yola, lokacin da yake gabatar da wani rahoto ga ayarin jami’an shirin noman Fadama a karkashin jagorancin Dokta Ben Herbert. Bello ya ce shirin Fadama Kashi na 3 (AFII), wanda ake kira shirin bayar da agajin gaggawa na samar da hanyoyin neman abinci da tsaro a yankin Arewa maso Gabas, an tsara shi ne domin magance matsalar rashin abinci da ya damu mutanen yankin, musamman ’yan gudun hijira.
Ya kara da cewa nasarorin da aka samu a shirin ya sa Gwamnatin Jihar ta biya wannan mukudan kudade domin ci gaban shirin. “Dalilin gudanar da ayyukan Fadama Kashi na 3 (AFII) a jihohi shida na yankin Arewa maso Gabas da suka hada da Borno da Yobe da Adamawa da Taraba da Bauchi da Gombe shi ne tabbatar da nagartar shirin. Jihar Adamawa na cikin jihohin da suke cin moriyar shirin, kuma ana sa ran cewa sama da iyalai 4,000 ne za su ci moriyar shirin a jihar a karshen shirin.
A cewar shugaban shirin na Fadama III (AFII), shirin ya kunshi kananan hukomomi 21 na jihar. Daga cikin iyalai 4,000 da za su ci moriyar shirin, mutum 2,240 sun dawo garuruwansu, kuma 1,760 mutane ne daga garuruwan da ake gudanar da shirin. Sannan shirin ya dauki masu gudanarwa guda 20 a fadin jihar. Ya ce shirin ya fadada tunanin wadanda suka ci moriyarsa kuma sun samu shawarwari. A bangaren noman hatsi, an tallafawa 2,331 a karkashin shirin, kuma an tallafa wa bangaren kiwon kifi.
Ya kara da cewa shinkafar da ta kai kilo 12,950 nau’i daban-daban aka raba, sannan an noma hekta 207 na shinkafa. Sauran hatsin da aka raba sun hada da masara da dawa, da gyada da albasa, kuma an raba takin zamani da maganin ciyawa da na kwari da sauransu. Kuma an ba iyalai 4,000 shawarwari a fadin jihar, wadanda suka hada da mutum 2,331 a bangaren noma da kuma 1,669 a bangaren kiwo.